FASALl NA DAYA |
Ayoyi Dangane da Mahadi: Ba boyayye ba ne cewa Alkurani da sunna tagwayen juna ne daga mai shari’a guda. Kuma akidar musulmi game da Mahadi a jejjere ta zo ta hanyoyi dabam-daban daga Annabi (S.A.W.A.) babu shakka kuma babu rikitarwa-kuma Alkur’ani ya riga ya karfafa su da ayoyi da dama wadanda masu Tafsiri da dama suka danganta su ga Mahadi da aka yi bushara game da bayyanarsa a karshen zamani.
ldan kuwa har wani abu ya zo daga Annabi (S.A.W.A.) ta hanyoyi dabam-daban a jejjere to kuwa babu yadda za a yi Alkur’ani ya yi masa rikon sakainar kashi Koda kuwa hankulanmu ba su fahince shi ba saboda fadar Allah Ta’ala:
“Kuma Mun saukar da Alkur’ani gare ka bayani ga dukan kome”. (Surar Nahli: 89.)
Saboda fito da wannan akida daga ayoyin sun ta’allaka ne ga wanda ya fahinci Alkur’ani fahinta ta gaskiya’Babu shakka cewa Ahlul Bait (A.S.) Su ne tagwan Alkur’ani da nassin “Hadis, saklaini wato hadisin Abubuwa Biyu masu nauyi wadda aka ruwaito ta hanyoyi dabam-daban a gurin dukan musulmi, dan haka abinda ya tabbata daga gare su (A.S.) wato Ahlul Bait a dangane da Mahadi babu makawa a karbe shi a amince da shi.
Dangane da haka mun gano hadisai da dama daga Ahlu Bait (A.S.) wadanda suke fassara ayoyi da dama da Imam Mahadi (A.S.). kuma ba za mu ambato daga cikinsu ba sai wadanda malaman Tafsirin Sauran Mazhabobi suka tabbatar da su, da sauran ruwayoyinsu.
1-Daga cikinsu akwai wadanda Za mu share fagen mukaddama da su da cewa: Lalle makiyan addinin nan daga Ahlil kitab da Munafukai da mushrikai da Mabiyansu: “Suna nufin dushe hasken Allah ne da bakunansu amma Allah ya ki sai dai ya cika haskensa koda mushirikai sun ki.” (Surar Taubat: 32.)
Wannan aya mai ban al’ajabi ta bayyana mana cewa halin Wadannan kamar halin Wanda yake son yahure haske ne mai yawa wanda ya yadu a kusurwoyi, da bakinsa, Allah kuma yana son ya kai shi kololuwar cika a haske da haskakawa. Acikin wannan maganar akwai matukar kaskantarwa dare su da wulakanta la’amarinsu da raunana makýircýnsu domin hurar bakin za ta iya dushe haske mai rauni ne kawai-Wato kamar hasken fitilar a-ci-fal fal, sam ba za ta taba iya hure hasken musulunci mai girma Mai karuwa ba.
Wannan yana daga cikin al’amuran ban al’ajabi game da bayanin Alkurani, kuma yana daga zurfafan surantawar abubuwa daga ubangiji, saboda abinda ya kunsa na kawo misali na kwarewa ainun wanda ya kai koli a bayani, ba za ataba samun makamancinsa ba a wanin Alkur’ani.
Sa’annan sai Alkur’ani ya biyar da bayani gare mu bayan wannan misalin cikakken nufin daukakar wannan addinin kome kinsu kuwa, Allah Ta’ala ya ce- “Shi ne wannan da ya Aiki Manzonsa da shiriya da kuma addini na gaskiya domin ya fifita shi a kan addini dukkaninsa koda Mushiri kai sun ki.” (Surar Taubat: 33)
Fadar Allah Ta’ala: “Domin ya daukaka shi a kan addinai baki daya” wato ya taimake shi a kan dukan addinai, lamirin nan da ke cikin “li yuz hirahu” wato domin “Ya daukaka shi.” Yana komawa ne ga addinin gaskiya a gurin Manyan mafassara da mashahuransu kuma sun sanya shi a matsayin abu mafi saurin bayyana a lafazin ayar.
Wannan bushara ce Mai’girma daga Allah Ta’ala ga Manzonsa (S.A.W.A.) da taimako ga wannan addinin da kuma daukaka kalmarsa, Wannan bushara ta hadu da ta’akidi a kan cewa manufar makiyan addini ta dushe hasken musulunci ba za ta taba rinjayar iradar Allah Ta’ala ta fifita addininsa madaidaici a kan Sauran addinai ko da Mushirikai sun ki ba.
Fifiko a Wannan ayar babu abinda ake nufi da shi face galaba da daukaka Razi ya ce a Tafsirinsa: “ka sani cewa daukaka ko bayyanar wani abu a kan wani yana iya zamantowa da hujja, kuma yana iya zama da yawan adadi da taruwa, kuma yana iya kasancewa da galaba da fifiko. kuma sananne ne cewa Allah Ta’ala ya yi bushara da haka kuma bai halatta a yi bushara da abu ba sai abinda Zai Zo nan gaba wanda bai auku ba, dauka-kar wannan addini da hujja abu ne tabbatacce kuma sananne, don haka abu da yake wajibi shi ne daukar sa a daukaka ta yin galaba.”[1]
Abu ne da ba Zai boyu ba cewa wannan galabar a kan sauran addi-nai ta tabbata a Zamanin Annabi (S.A.W.A.) kuma mafificin dalili a kan haka shi ne cewa sun bayar da jiziya ga musulmi da hannunsu suna kaskantattu kuma ba zai boyu ba cewa wannan galabar da nasarar ta kasance ne da abinda ya dace da zamantowar musulunci a matsayinsa na addini Mai karfi, wanda ke da garkuwa ko ta wane gefe.
Sai dai halin da muke ciki a yau ba haka yake ba, wadanda suka ba mu jiziya a jiya yau sun kankane mana abubuwan da muke tsarkakewa, makiya kuma sun yi mana kawanya, an yake mu a cikin gidajenmu, tare kuma da abinda ake gani a sarari na yada addinin Ma’abuta littafi, (yahudu da Nasara) kuru-kuru.
ldan har mun kasance mun yi imani da cewa Alkur’ani Shi ne kyautuwar yau da gobenmu, shin ma’anar bayyana da fifitar wannan addinin a kan sauran addinai ta yi daidai da halin da musulunci yake ciki a yau alhali yana kusa da zamantowa a kayyade da kungiyoyin musulmi da siyasoshinsu?
Abu guda da ya tabbata a busharar nan shine kawai ganin mutane masu yawa da ke danganta kansu da musulunci a yau duk kuwa da abinda ke cikinsu na sabani da tuka da warwara da bam-bancin akida da hukunce -hukunce? Wannan kuwa duk da cewa abinda aka ruwaito daga katada ta game da fadin Allah Ta’ala: “Domin ya fifita shi a kan addinai dukansu” ya ce: “su ne addinai guda shida: wadanda suka yi imani, da wadanda suka yahudaance, da sabi ’awa da Nasara da Majusu da kuma wadanda suka yi shir ka. Don haka duk addinai za su shiga karka-shin addinin Muslunci shi ma kuma musulunci ya shiga wani sashe daga cikinsu, dan haka Allah ya zartar da hukunci kuma ya saukar da cewa zai daukaka addininsa a -- kan addinai dukkaninsu koda mushirkai sun ki.”[2]
A Tafsirin lbin Jazziy kuwa: “Daukaka shi kuwa: shi ne sanya shi mafi daukakar addinai kuma mafi karfinsu har ya game Gabashi da yammaci.”[3]
A Durrul Mansur: “sa’id bin Mansur da lbin Mansur da - Baihaki a sunani daga Jabir (R.A) game da Fadin Allah Ta’ala Cewa”. Domin daukaka shi a kan addinai dukkaninsu ya ce: “Ba zai Zamanto haka ba har sai ya zamanta babu Bayahude ko Banasare mai wani addini sai musulunci.[4]
Daga Mikdad Bin Aswad ya ce: “Na ji Manzon (S.A.W.A.) yana cewa: Babu wani gidan Marmara ko kankare da zai saura a bayan kasa face kalmar Musulunci ta shige shi, ko da daukaka madaukaki ko kuma da kaskanci mai kaskantarwa. Ko ya daukaka su sai Allah ya sanya su cikin Ma’abutansa su daukaka da shi ko kuma ya kaskan tar da su su yi addini da shi.”[5]
Daga nan ne kuma ya zo a hadisi daga Imam Bakir (A.S.) cewa ayar tana Bushara ne game da bayyanar Mahadi (A.S.) a karshen Zamani, kuma cewa da taimako daga Allah -zai daukaka addi-nin kakansa a kan sauran addinai har ya zamanto babu wani mushiriki da zai saura a bayan kasa, wannan shi ne maganar Siddiy malamin[6] tafsiri.
Kurtubiy ya ce: “Siddiy ya ce wannan lokacin bayyanar Mahadi ke nan, babu wani wanda zai saura face ya shiga musulunci.”[7]
-2- Daga cikinsu akwai: Fadin Allah Ta’ala:
“Kuma da za ka gani yayin da suka firgita, to babu kubuta sa’an nan aka kama su daga guri makusanci.” (Surar Saba’i: 34 -51)
Tabari ya kawo a tafsirinsa daga Huzaifah Binul yaman tafsirinta a kan sojojin da za a kife kasa da su, bayanin abinda zai nuna cewa wannan kife kasar bai auku ba tukuna zai zo nan gaba da kuma ruwaito da aka yi daga littafa ingantattu da Madogarai amintattu, kuma da cewa yana daga cikin alamun tashin duniya da ke hade bayyanar Mahadi ba tare da wani sabani ba.[8]
Da kuma abinda Tabari ya kawo wanda kurtubi ya ambata shi a littafin “Tazkirah” kai tsaye daga Huzaifah Binul yaman, kuma da shi Abu Hayyan ya bayyana a sarari a Tafsirinsa, da kuma Makdisi Basha-fi’e a littafin Akdid Durar, da kuma suyuti a Al-Hawiy lil Fattawiy, kuma Zamakhshari ya kawo shi a Tafsirinsa kasshaf daga lbin Abbas, Tabrisi ya ce a Majma’ul Bayan: Sa’alabiy ya kawo shi a Tafsirinsa, mutanenmu ma sun kawo makamancinsa a hadisan Mahadi (A.S.) daga Abiy Abdillah (A.S.) da Abiy Ja’afar (A.S.).[9]
3- Daga cikinsu akwai Fadin Allah Ta’ala: “Kuma lalle shi tabbas wani ilimi ne na sa’a, sabida haka kada ku yi shakka game da ita kuma ku bi ni. Wannan ita ce hanya madaidaiciya.” (Surar Zukhruf: 61)
Bagawiy ya bayyana karara a tafsirinsa, da kuma Za makhshariy, da Razi kurtubiy, da Nafsiy, da khazin, da Tajuddinil Hanafiy, da Abu Hayan da lbin kasir, da Abu Sa’ud, da Haisamiy, cewa ayar kebantacciya ce game da saukowar Annabi lsa dan Maryama (A.S.) a karshen Zamani.[10]
A Durrul Mansur Suyutiy yayi ishara ga abinda Ahmad Bin Hanbal da lbin Abi Hatam da Tabaraniy, da lbin Mundawayhi, da Faryabiy, da sa’id bin Mansur, da Abdu bin Humaid suka kawo daga hanyoyi da bam-daban daga lbin Abbas cewa ita ta kebanta da abinda Muka ambata ne.[11]
Alkanjiy As-Shafi’iy ya fadi a cikin littafinsa Al-Bayan cewa: “Mukatil bin Sulayman da wanda ya bi shi daga masu Tafsiri Sun ce a Tafsirin Fabdin Allah kuma lalle tabbas ’shi wani ilimi ne na sa’a.” Shi ne Mahadi (A.S.) Zai kasance a karshen Zamani bayan bayyanarsa tashin duniya da alamunta za su zo.”[12]
Za ka iske kwatankwacin wannan bayanin karara a gurin lbin Hajar Haitamyi da shabalanjiy As-shafi’iy, da Saffariniy Al-Hanbaliy, da kanduziy Al-Hanafiy, da Sheikh sabban.[13]
Babu sabani a tsakanin wadannan da wadancan domin saukar Annabi lsa (A.S.) za ta kasance ne hade da bayyanar Mahadi (A.S.) kamar yadda ya zo a sahih Bukhari da sahih Muslim da sauran littafan Hadisai kamar yadda za mu bayyana a fasali na uku na wannan bayanin. Dogaro da isharorin wasu da muka ambata wadanda suka fayyace haka a sarari sun kawo daga tafsirin Sa’alabi cewa shi ya kawo a tafsirin wannan aya daga lbin Abbas da kuma daga Abu Huraira da katadata, da Malik Bin Dinar da Dahhaku abinda ke nuna cewa dangane da saukowar Annabi lsa dan Maryama (A.S.) tare kuma da nunawa a sarari game da samuwar Mahadi (A.S.) da kuma Cewa Zai yi salla a bayan Mahadi (A.S.).
4-Daga cikinsu akwai fadar Allah Ta’ala: “Ba sai Na yi rantsuwa da taurari Masu tafiya da baya-da baya ba, Masu gudu masu buya.” (Surar Takwi:81:15)
Ya zo a hadisi daga Imam Bakir (A.S.) cewa ya ce: “Imam yana boyuwa shekaru dari biyu da sittin sa’an nan ya bayyana kamar walkiya yana haskaka dare mai duhu, idan har ka riski zamaninsa to idonka zai yi sanyi.”[14]
Ba zai boyu ba cewa wannan hadisi ne gagara ba dau wanda AhlulBaiti (A.S.) suka same shi daga Annabi (S.A.W.A.) wanda shi kuma ya same shi ta wahayi daga Allah mabuwayin sarki.
Za mu wadatu da wannan gwargwa-do haka saboda cewa shaikh kanduziy ya kawo ayoyi da dama da lmaman Ahlul Bait (A.S.) suka fassara su da Imam Mahadi (A.S) da kuma bayyanar-sa a karshen Zamani. [Yanabi’ul Mawadda 3: 76-85 a Babi na 71].
Nazari ko da sau daya a kan hadisan da suka zo a littafan Musulmi game da mahadi (A.S.) zai gamsar da kasancewarsu cewa sun Zo ta hanyoyi dabam-dabam daga mutane dabam-daban daga Annabi (S.A.W.A.) ba tare da jin wani shakku ba. Da yake wannan bincike ba zai iya wadatar, wa mu kawo dukan hadisan da aka ruwaito a littafan Musulmi game da Mahadi (A.S.) ba saboda tsananin yawan da suke da shi don haka za mu takaita a kan ambata abinda ke ba da tabbacin ruwaito hadisan mahadi (A.S.) daga Annabi (S.A.W.A.) kamar haka:-
Fadin cewa babu wani malamin hadisi daga Malaman hadisin Musulunci face ya kawo wasu hadisai da ke albishir game da bayyanar Imam Mahadi (A.S.) a karshen Zamani ba zai Zama karin gishiri ba, har ma sun ware littafa da dama a kebe[15] game da Imam Mahadi (A.S.).
Amma dangane da malamai da masu hadisan da suka kawo hadisan Imam Mahadi (A.S.) ko kuma suka ruwaito su daga wadanda suka gabace su a bisa salon kafa hujja da ita kamar yadda muka ga haka a littafansu su ne kamar haka:-lbin Sa’ad Mai Littafin Tabakatul kubra (Wanda ya yi wafati a shekara ta 230 Hijiriyya) da lbin Abi shaybah [Wanda ya yi Wafati a shekara ta 235 Hijiriyya], da Ahmad bni Hanbal [Wanda ya yi wafati a shekara ta 241 Hijiriyya] da Bukhriy [Wanda ya yi wafati a shekara ta 256 Hijiriyya] ya ambata Mahadi (A.S.) da siffa ne ba da suna ba, Muslim ma (wanda ya yi wafati a shekara ta 261 Hijiyya) ya aikata kamar yadda ya yi a littafinsa Sahihu muslim kamar yadda Za mu bayyana a Fasali na uku a wannan littafin, da kuma Abubakar Askafiy (wanda ya rasu a shekara ta 260 Hijiriyya) da lbin majan (wanda ya rasu a shekara ta 273 Hijiriyya) da Abu Dawud (wafatinsa shekara ta 275 Hijiriyya) da lbin kutaiba Ad-dainawari (wafatinsa 276 Hijiriyya) da Tirmizi (wafatinsa shekara ta 279 Hijiriyya) da Bazariy (wafatinsa shekra ta 292 Hijiriyya), da Abu ya’ala musiliy (wafatinsa shekara ta 307 Hijiriyya) da Tabariy (wafatinsa shekara ta 310 Hijiriyya) da Akiliy (wafatinsa shekara ta 322 Hijiriyya) da Na’im Bin Hamid (wafatinsa shekara 328 Hijiriyya) da shaikhul Hanabila, wato shugaban ’yan Hamba-liyya a zamaninsa, Barbahriy (wafatinsa shekara ta 329 Hijiriyya) a littafinsa sharhus sunna da kuma lbin Habanal Bastiy (wafatinsa shekara ta 354 Hijiriyya) da makdisiy (wafatinsa shekara 355 Hijiriyya) da Tabaraniy (wafatinsa shekara ta 360 Hijiriyya) da Abu Hasan Abiriy (wafatinsa shekara ta 363 Hijiriyya) da Darul kutuniy (wafatinsa shekara ta 385 Hijiriyya) da khattabiy (wafatinsa shekara ta 388 Hijiriyya) da Hakim Naisaburiy (wafatinsa 405 Hijiriyya) da Abu Na’im lsfahaniy (wafatinsa shekara ta 430 Hijiriyya) da Abu Amrud Daniy (wafatinsa shekara ta 444 Hijiriyya), da Baihakiy (wafatinsa shekara ta 458 Hijiriyya) da khatib Bagdadiy (wafatinsa shekara ta 463 Hijiriyya) da lbin Abdulkarim malikiy (wafatinsa shekara ta 509 Hijiriyya)da Al-Baghawiy (wafatinsa shekara ta 510 ko 516 Hijiriyya) da A-kali lyadh (wafatinsa shekara ta 544 Hijiriyya) da khowari Zamiy Al-Hanafiy (wafatinsa shekara ta 597 Hijiyya) da lbin Jauziy (wafatinsa shekara ta 606 Hijiriyya) da lbin Arabiy (wafatinsa shekara ta 638 Hijiriyya) da muhammad bin Talha As-Shafi’iy (wafatinsa shekara ta 652) da Allama sibti lbin Jawziy (wafatinsa 597 Hijiriyya) da lbin Abil Hadid Al-mu’utaziliy Al-Hanafiy (wafatinsa shekara ta 655 Hijiriyya) da Al-munziriy (wafatinsa shekara ta 656) Hijiyya) da Al-kinjiy Al-shafi’iy (wafatinsa shekara ta 658 Hijiriyya)da kurdubiy Al-malikiy (wafatinsa shekara ta 671 Hijiriyya) da lbin khalkan (wafatinsa shekara ta 681 Hijiriyya) da muhibbuddin At-Tabariy (wafatinsa shekara ta 694 Hijiriyya) da Allama lbin manzur (wafatinsa shekara ta 711 Hijiriyya) a lafazin HADIYA na lisanal (Arab) da lbin Taymiyya (wafatinsa shekara ta 728 Hijiriyya) da Ala’uddin Bin Balban (wafatinsa shekara ta 739 Hijiriyya) da Juwiniy As-Shafi’iy wafatinsa shekara ta 730 Hijiriyya) da waliyuddin Al-Tabriziy (wafatinsa shekara ta 741 Hijiriyya) da Al-Maziy (wafatinsa shekara ta 739 Hijiriyya) da zahbiy (wafatinsa shekara ta 748) da lbin Wardiy (wafatinsa shekara ta 749 Hijiriyya) da zarandi Al-Hanafiy wafatinsa shekara ta 750 Hijiriyya) da lbin kayyim Al-Jawziy (wafatinsa shekara 751 Hijiryya) da lbin kasir (wafatinsa shekara ta 774 Hijiriyya) da Sa’aduddin Taftazaniy (wafantisa shekara ta 793) da Nuraddin Al-Hisamiy (wafatinsa 807 Hijiriyya) da lbin khaldun Al-magribi (wafatinsa shekarata 808 Hijriyya) shi ne wanda ya tabbatar da ingancin hadisai hudu game da Mahadi (A.S) duk da matsayinsa da aka sani wanda kuma zamu kawo bayaninsa a Fasali na uku, da kuma shaikh muhammad Jawziy Ad-Dimashkiy As-Shafi; iy (wafatin shekara ta 833 Hijiriyya) da Abubakar busiriy (wafatinsa shekara ta 852 Hijirjiyya) sakhawiy wafatinsa shekara ta 902 Hijiriyya) da suyutiy (wafatinsa shekara ta 911 Hijiriyya) da sha; araniy (wafatinsa shekara ta 973 Hijiriyya) da lbin Hajar Al-Haitamiy (wafatinsa 974 hijiriyya) da muttakiy Al-Hindiy (wafatinsa 974 Hijiriyya) da dai sauransu, daga cikin malaman baya-bayan nan kamarsu shaikh mar’iy Al-Hanbaliy (wafatinsa shekara ta 1033 Hijiriyya) da Muhammad RasuL Al-Barzanjiy (wafatinsa shekara ta 1108 Hijiriyya) da Zarkaniy (wafatinsa shekara ta 1122 Hijiriyya) da muhammad lbin kasim Al-Fakihi Al-Malikiy (wafatinsa shekara ta 1182 Hijiriyya) da Abil Ala Al-lrakiy Al-Magribiy (wafatinsa shekara ta 1183 Hijiriyya) da SaHariniy Al-Hanbaliy (wafatinsa shekara ta 1188 Hijiriyya), da zabidiy Al-Hanafiy (wafatinsa shekara ta 1205 Hijiriiyya) a littafin (Tajul Arus) gurin kalmar “Hadiy”, da shaikh sabban (wafatinsa shekara ta 1206 Hijiriyya) da muhammad Amin AS-Swidiy (wafatinsa shekara ta 1246 Hijiriyya)da shaukaniy (wafatinsa shekara ta 1250 Hijiriyya) da Mumin shabalanjiy (wafatinsa shekara ta 1291 Hijiriyya) da Ahmad zainiy Dahlaniy Al-Fakih wal muhandi’s As-Shafi; iy (wafatinsa shekara ta 1304 Hijiriyya) da Sayyid muhammad Sadik Al-Kanujiy Al-Bukhariy (wafatinsa shekara ta 1307 Hijiriyya) da shuhabuddin Al-Halawaniy As-shafi’iy (wafati shekara ta 1308) da Abil Barakat Al-Alusiy Al-Hanafiy (wafati shekarata 1317 Hijiriyya) da Abi Tayyib muhammad shamsul Hakk Alzimabodiy (wafati shekara ta 1329 Hijiriyya) da kattaniy Al-malikiy (wafati shekara ta 1345 Hijiriyya) da mubarakFuriy (wafati 1353 Hijiriyya) da sheikh mansur Ali Nasif (wafatinsa bayan shekarar 1373 Hijiriyya) da shaikh muhammad khidr Husain Al-Misriy (wafati 1377 Hijiriyya da Abi Faiz Gamari As-shafiliy (wafati shekara ta 1380 Hijiriyya) da Fakihi Al-kasim Binjid shaikh muhammad Bim Abdil Aziz Al-mani’u (wafati shekara ta 1385 Hijiriyya) da shaikh muhammad Fu’ad Abdul Bakiy (wafatisa shekara ta 1388 Hijiriyya) da Abul Aa’la maududiy da Nasiruddin Al-Albaniy zuwa illa masha Allah na daga cikin malaman wannan zamanin, idan kuma muka kara malaman Tafsiri daga Ahlussunna kamar yadda ishara ta gabata a kan haka to ya rage naka ka kintata gwargwadon ittifakin da ake da shi a kan ruwaito hadisai game da Imam mahadiy (A.S.) da kuma kafa dalili da su.
Dangane da malaman shi’a da masanan hadisansu da masu fassara wadanda suka kawo hadisai game da Mahadi (A.S.) za a samu damar ambata sunayensu ne kawai saboda kasancewar yin imani da bayyanar Imam mahadi daga cikin jiga – jigan, akidunsu.
Lalle sahabban da suka ruwaito hadisai game da Mahadi daga manzon Allah (S.A.W.A.) ko kuma wadanda suka kasance hadisansu sun takaitu da su kawai amma hukuncinsu hukuncin isa har zuwa ga Annabi (S.A.W.A.) ne, -saboda ba zai dace da hankali ba a ce su suka yi hukuncin kansu a wannan, -suna da yawan gaske, idan har ruwaitowa ta tabbata daga kashi daya daga cikin gomansu to, tawaturanci, wato yawan hanyoyin ruwaitowa ta tabbata babu shakku kuma babu rikitarwa, kamar yadda ya zo a madogaran Ahlussunna kawai su ne:-
Fatumatuz zahra (A.S.) (wafati shekara ta 11 Hijiriyya) da mu’azu Bin Jabal (wafati shekara ta 18 Hijiriyya) da Katadata Bin Nu’aman (wafati shekara ta 23 Hijiriyya) da Abu ZaruL Ghifariy (wafati shekara ta 32 Hijiriyya) Abdullahi Bin mas ’ud (wafati shekara ta 32 Hijiriyya) da Abbas Bin Abdul mutallib (wafati shekara ta 35 Hijiriyya) da salmanul Farisiy (wafati shekara ta 36 Hijiriyya da Talha Bin Abdullah (wafati shekara ta 36 Hijiriyya) da Ammar Bin yasir (wafati shekara ta 37 Hijiriyya) da Imam Ali (A.S.) (wafati shekara ta 40 Hijiriyya) da Tamimud Dariy (wafati shekara ta 50 Hijiriyya) da Abdurrahman Bin Sumra (wafati shekara ta 50 Hijiriyya) da lmran bin Hasin (wafati shekadra ta 52 Hijiriyya) da Abu Ayyub Al-Ansariy (wafati shekara ta 52 Hijiriyya) da Sauban Fansar Annabi (S.A.W.A.) (wafati shekara ta 54) da kuma UmmiL Muminina A’isha (wafati shekara ta 58 Hijiriyya) da Abu Huraira (wafati shekara ta 59 Hijiriyya) da Imam Husain (A.S.) (shahada shekara ta 61 Hijiriyya) da Ummu Salama (wafati shekara ta 62) da Abdullahi Bin umar Binulkattab (wafati shekara ta 65) da Abdullahi lbin Amr Binul As (wafati shekara ta 65 Hijiriyya) da Abdillah Bin Abbas (wafati shekara ta 68 Hijiriyya) da zaidu Bin Ar kam (wafati shekara ta 68 Hijiriyya) da Awf Bin malik (wafati shekara ta 73 Hijiriyya) da Abu sa’iduL khudriy (wafti shekara ta 74 Hijiriyya) da Jabir Bin sumra (wafati skekara ta 74 Hijiriyya) da Jabir Bin Abduillahil Ansariy (wafati shekara ta 78 Hijiriyya) da Abdullahi Bin Ja’afar At-Tayyar (wafati shekara ta 80 Hijiriyya) da Abu Hamamatal Bahiliy (wafati shekara ta 81 Hijiriyya) da Bashar Binul Munzir Binul Jarud (wafati shekara ta 83 Hijiriyya) an yi sabani a kansa, an ce mai ruwaya ne kuma kakansa shi ne Jarudiy Bin Amru (wafati shekara ta 20 Hijirin) da Abdullahi BinuL Haris Bin Jaz’uz zubaidiy (wafati shekara ta 86 Hijiriyya) da sahal Bin sa’adus sa’idiy (wafati shekara ta 91 Hijiriyya) da Anas Bin Malik (wafati shekara ta 93 Hijiriyya) da Abut Tufail (wafati shekara ta 100 Hijiriyya) Da sauransu wadanda ban samu ainihin tarihin rasuwarsu ba kamarsu Ummu Habiba, da Abil Jahhf, da Abi salma makiyayin manzon Allah (S.A.W.A.), da Abi Laila, da Huuzaifa Binul yaman, da Harsi Binu Rabi’u Abi katadata da zarry Bin Abdillah da zurara Bin Abdillah da Abdullahi Bin Abi Awfa da Ala’a, da Alkamata Bin Abdillah da Aliyul Hilaliy da kurrata Bin Ayas.
Na uku: Hanyoyin Hadisan Mahadi (A.S.) a littafan sunna A Dunkule:sayyid Ahmad Bin muhammad Bin sadik Abul Fai z Al-Gamariy Husain As-shati’i y Al-magribiy malamin Al-Azhar (wafatinsa shekara ta 1380 Hijiriyya ya kokarta kuma ya amfanar a litta-finsa muhinmi; mai suna “lbrazul wahmil maknun min kalami lbin khaldun” wata “Bayyana wahamin da ke Akwai amaganar lbin khaldun” inda ya tabbatar da hanyoyin ruwaitowar hadisin Imam Mahadi (A.S.) ta yadda babu wani da ya gabata da haka kafin Shi,wannan kana ya yi shi ne ta kure raunin lb in khaldun da wasu daga cikin malaman da suka yi zamani da shi kamarsu Ahmad Amin daga masar da farid wajadiy da sauransu suka fake da shi. A nan babu laifi mu dan tsawaita kadan. a kan hanyoyin hadisan Mahadi (A.S.) a littafan sunna da aka bayyana filla-filla a wannan littafin, wanda ke bayanin kwarewa wajen binciken hanyoyin ruwaya da madogarar hadasai game da Imam Mahadi (A.S.) daga littafan Ahlussunna farawa daga kan sahabbai sa’annan Tabi’ai sa’an nan Tabi’an Tabi’ai da kuma sarwa zuwa kan wanda ya fito da wannan hadisi daga cikin malaman hadisi.
Abul Faiz ya ce: “Ba zai boyu ba cewa al’ada ta hukunta koruwar daidaituwar jama’a da adadinsu ya kai talatin zuwa sama shi ne abinda ya iso gare mu kuma muka iya tabbatar da shi a halin yanzu, kuma mun rigaya mun samu hadisin mahadi (A.S.) ya zo daga hadisin Abi Sa’idul Khudriy, da Abdullahi Bin Mas’ud, da Aliyu Bin- Abi Talib, da ummu salama, da Sauban, da Abdullah Bin Taz’i Bin Harisuzzabidiy da Abi Huraira, da Anas Bin malik, da ummu Habiba, da Abiy umama, da Abdullah Bin Amru Binul As, da AmmarBin yasir da Abbas Bin Abdulmutallib, da Husain Bin Ali da Tamimud Dariy, da Abdur Rahman Bin Awf, da Abdullahi Bin umar BinuL khattab da Talha da Aliyul Hilaliy, da lmran Bin Húsain da Amru Bin marratal Jahaniy, da mu’az Bin Jabal, daga cikin mursal kuwa wato wa-danda suka dakata a kan maruwaitan su ya su, akwai:shahu Bin Haushan. Wannan abinda muka amkbata marfu’i ne kawai bamu ambaci maukufi da maktui ba wanda su ma a wannan babin tamkar marfui su ke.
To idan da za mu bi lalle da mun ambaci adadi mai yawa daga ciki, saidai kuma muna ganin cewa marfui da muka ambata ya wadatar.[16]
Na ce: Na ambata wannan ne kawai saboda a san cewa abinda ya tsere wa sayyid Abul Faiz Gamariy daga cikin sunayen sahabban da suka ruwaito hadisan Imam Mahadi (A.S.) ya fi yawan adadin da ya ambata domin ya ambata ashirin da shida ne kawai daga sahabbai a ciki har da Bin Haushabs bai ambata ashirin da takwas ba wadanda su ne:
Abu Ayyubal Ansariy da Abu Jahhaf, da Abu zarrilghifariy,da Abu salmiy Ra’iy Rasululluh (S.A.W.A.) da Abu wa’ih da Jabir Bin sumra, da Jarud Binur Rabin da Imam Hasan (A.S.) da zuran Bin -Abdullah da zurara Bin Abdullah da zaid Bin Arkam da zaid Bin sabit da sa’ad Bin malik, da salmanul Farsiy, da sahal Bin sa’adiy, da Abdurrahman Bin sumrata da Abdullahi Bin Ja’afarut Tayyar, da usman Bin usman, da Ala’u da Alkamata Bin Abdullah, da Umar Binul khattab, da Auf Bin malik, da majma BinJariya, da mu’az Bin Jabal kuma shi yana daga cikin sahabban Farko da suka ruwaito hadisan Mahadi (A.S.) kuma shi ya rasu ne tun shekara ta goma sha takwas (18) Hijiriyya ko ta halin kakadai, shi dai Abul Faiz Al-Gamariy As-shafi’iy ya bibiyi hadisan Mahadi (A.S.) wanda sahabbai sama da talatin suka ruwaito yana bayyana wadanda suka ruwaito daga cikinsu da kuma wanda ya kawo su daga cikin malaman hadisai; tare da dukkan tantancewa da fayyacewa.
Kuma da sannu za mu takaita a kan abinda ya fada game da hadisin Abi Sa’idil Khudriy kawai, wanda shi ne sahabi na farko da Abul Faiz ya ambace shi, sa’an kuma ka auna sauran hadisan sahabban.
Ya ce:
“Amma hadisin Abi Sa’idi Khudriy ya zo daga gare shi ta hanyar: Abi Nazrata da Abis Sadikil Najiy da Hasan Bin Yazid As-Sa’adiy.
Amma hanyar Abi Nazarata:
Abu Dawud ya kawo shi da Hakim, kuma dukansu su biyun daga ruwayar lmran kattani, daga gare shi kuma muslim ya kawo shi a littafin Sahih muslim daga Sa’id Bin Zaid da kuma daga ruwayar Dawud Bin Abi Hind kuma duka su biyun daga gare shi. sai dai a sahih muslim an ambata shi ne da sifa ba da suna ba kamar yadda zai zo.
Amma Hanyar Abis siddikun Najiy daga Abi sa’id kuma:
Abdurrazak ya kawo shi da Hakim daga ruwayar Mu’awiya Bin Karrah daga gare shi, kuma Ahmad da Tirmizi da lbin majah da Hakim sun kawo shi daga ruwayan zaydil Amiy, daga gare shi. Ahmad da Hakim sun fito da shi daga ruwayar mataru Bin Tahman da Abiy- Haruna Abadiy duk su biyun daga gare shi. Ahmad ya kawo shi kawai daga ruwayaa matar Bin Tuhman shi kadai daga gare shi. Har ila yau kuma ya kawo shi daga ruwayar Ala’a Bin Bashir Al-mazaniy daga gare shi kuma har ila yau ya kawo shi daga ruwayar matraf daga gare shi.
Tabaraniy ya kawo shi a Al-Awsat daga ruwayan Abi Wasil Abdu Bin Hamid daga Abis saddikun Najiy daga gare shi”.[17]
Na ce: ldan da za ka koma ga tarihin lbin khaldun Lalle da ka same shi cewa bai san wadannan hanyoyin hadisin Abi Sa’id ba sai kadan, ballantana ma abubuwan da ya bari daga tarihin sahabbai.
Ba zai boyu ba cewa gwargwadon abinda aka hadu a kansa a dukan hanyoyin nan zuwa kan hadisin Abi Sa’idul khudriy kawai banda sauran da ba shi ba, abinda aka hadu a kai, shi ne bayyanar Imam mahadi (A.S.) a karshen zamani, kuma babu shakka cewa duba dukan hanyoyin da suka zo da hadisan Mahadi (A.S.) daga dukan sahabbai na tabbatar da tabbaci da kuma jejjeruwar abinda Annabi (S.A.W.A.) ya yi albishir da shi kai hatta ma ko da mun kaddara cewa ta hanya daya ce aka ambata ga dukan sahabban to ta wadatar wajen tabbatar da yawan maruwaitansa kuma ya rigaya gabata cewa adadinsu ya fi hamsin. Na Hudu: lngancin HadisiGame da Mahadi: A nan za mu ambata wasu daga cikin masanan Ahlussunna ne wadanda suka bayyana ingancin hadisai game da Imam Mahadi (A.S.) kamar yadda muka samu a rubuce rubucensu, kuma ba wai manufarmu ita ce kididiga ba sai dai kawai ba da misalan abinda aka yi imani da shi kamar haka:-
1- Imam Tirmizi (wafati shekarata 297 Hijiriyya) ya ce game da hadisai uku dangane da Imam Mahadi ( A.S.) wannan Hadisi ne mai kyau ingantacce"[18]
2- Hafiz Abu Ja’afar Akiliy (wafati shekara ta 322 Hijiriyya) ya kawo hadisi rarrauna game da Imam Mahadi (A.S.) sa’an nam ya ce:-“Game da Mahadi kuma akwai hadisai kya-wawa ba ta wadannan fuskar ba sabanin wannan lafazin.” [19]
3- Hakim Naisaburiy (wafati shekara ta 405 Hijiriyya) ya ce dangane da hadisai hudu, wannan hadisi ne mai ingantaccen isnadi amma ba su fito da shi ba.
4- Dangane da hadisai uku kuwa: “Wannan hadsi ne mai inganci a bisa sharadin muslim amma ba su fito da shi ba.” [20]
Dangane da wasu hadisai guda takwas kuwa ya ce: “Wannan hadisai ne ingantattu a bisa sharadin Buhari da muslim amma ba su fito da shi ba.”[21]
Imam Baihakiy (wafati shekara ta 458 Hijiriyya) ya ce: “Kuma hadisai game da bayyanar Imam Mahadi su ne mafiya ingancin isnadi.”
5- Imam Bagawiy (wafati shekara ta 510 ko 516 Hijiriyya) Ya fito da hadisi game da Mahadi (A.S.) a fasalin sihah da kuma wasu hadisan kuma guda biyar dangane da shi, a Fasalin Hasanat daga littafin “Masabihus Sunna”.
6- lbin Asir (wafati shekara ta 606 Hijiriyya) A littafin, (Nihaya) ya kawo a lafazin “Hada” kuma daga ciki akwai hadisi: Sunnar Halifofi shiryayyu masu shiryarwa Mahadi: Wanda Allah ya shirye shi zuwa ga gaskiya kuma anyi amfani da shi a sunaye har sai da ya zamanto kamar yawancin sunaye kuma da shi ne aka sanya Mahadi wanda manzon Allah (S.A.W.A.) ya yi albishir game da shi cewa zai zo a karshen zamani.[22]
Wannan magana ce da ba za ta zo ba sai daga wanda yake ganin ingan-cin hadisai game da Mahadi kai hatta ma zuwansu ta hanyoyin ruwaya da dama dabam-daban a bisa batu mafi inganci.
7- Kurtubi maliki (wafati shekara ta 671 Hijiriyya) yana cikin masu ikrari da kawo wannan hadisin ta hanyoyi dabam-daban. Abu mai muhimmanci a gare mu a nan shi ne cewa game da hadisin Mahadi daga lbin majah cewa ya yi: “lsnadinsa ingantacce ne.” ya kuma bayyana a sarari cewa “Mahadi daga cikin zuriyata ne daga ’ya’yan Fatima kuma shi ne ya fi hadisin muhammad Bin khalidul Jundi wanda za mu daldale shi daga bisani.
8- lbin Taimiyya (wafati shekara ta 728 Hijiriyya) ya ce a littafin minhaijus sunna: “Lalle hadisan da yake kafa hujja da su -wato Allama Hilli-game da bayyanar Mahadi hadisai ne ingantattu.”[23]
9- Hafiz zahbi (wafati shekara ta 748 Hijiriyya) ya yi shiru game da dukan hadisan da Hakim ya tabbatar da ingancinsu a littafin mustadrak dinsa dangane da hadisan Mahadi yana mai bayyana ingancin hadisai biyu, ya kuma yi raddin a kan wasu daga cikin wadanda Hakim ya tabbatar da ingancinsu daga hadisai game da abinda Hakim ya ingantar yana fassara yardarsa game da ingancin haka.
10- Al-Kinji Shafi’i (wafati shekara ta 658 Hijiyya) ya ce game da hadisin da Tirmizi ya kawo kuma ya inganta shi game da Mahadi (wannan Hadisi ne sahihi) dangane da wani kuma makamancinsa ya ce game da hadisin “Mahadi daga gareni yake mai hasken fuska” “wannan hadisi ne tabbtacce mai kyau kuma ingantacce.”[24]
11- Hafiz lbin kayyim: (wafati shekara ta 751 Hijiriyya) ya yi ikrari game da ingancin wasu daga cikin hadisan Mahadi da kuma game da ingancin wasunsu daban bayan ya kawo wani daki daga cikinsu, lbin kayyim kuwa yana daga cikin masu tabbatar da tawaturancin hadisai masu yawan hanyoyin ruwaya, kamar yadda zai zo nan gaba.
12- lbin Kasir (wafati shekara ta 774 Hijiriyya) ya ce game da isnadin wani hadisi game da Mahadi “wannanciro isnadi ne mai karfi ingantacce.”[25] Sa’an nan kuma sai ya wani hadisin daga lbin majah ya ce : wannan hadisi ne mai kyau kuma an kawo shi ba ta fuska daya ba daga Annabi (S.A.W.A.)”.[26]
13- Taftazani (wafati shekara ta 793 Hijiriyya) ya ce game da bayyanar Mahadi a karshen zamani “Lalle hadisai ingantattu sun zo game da wannan Babin.“
14- Nuruddin Haisami: (wafati shekara ta 807 Hijiriyya) ya kawo wasu adadin hadisai game da Imam Mahadi (A.S.) sa’an nan ya yi ikrari game da ingancinsu da yarjewa da maruwaitansu.
Ya ce game da dayansu "Tabarani ya ruwaito shi a Al Ausat da kuma littafinsa na Rijal wato "Rijal" na Sihah".
Game da waninsu kuma ya ce: “Na ce Tirmizi da kuma waninsasun ruwaito shi a takaice sosai Ahmad ma ya ruwaito shi da hanyoyi, da kuma Abu ya’ala a takaice matuka, kuma mazajensu amin-tattu ne.”
Game da na uku kuwa cewaya yi: “AL-Bazaru ya kawo shi, maruwaitansa kuwa ingantattu ne.”
Game da na biyar kuma ya ce “Tabarani ya ruwaito shi a Al-Awsat, mazajensa kuma amintattu ne.”
15- Suyuti (wafati shekara ta 911 Hijiriyya) ya yi wa wasu hadisai da aka ruwaito game da Mahadi (A.S.) alama da (Sah) wato ma; ana Sahihi, ga wasunsu kuma (h) wato hasanun ma’ana mai kyau ne!
16- Shaukani (wafati shekara ta 1250 Hijiriyya) kanuji ya kawo daga gare shi da batunsa game da ingancin hadisan Imam Mahadi (A.S.) kai hatta ma da tawaturanci” ya gabata cewa ya rubuta littafi game da tawaturancin Mahadi (A.S.).
17- Nasiruddin Albani: Ya ce a wata makala tasa mai suna: “Game da Mahadi wanda nassinsa shi ne”. “Amma al’amarin Mahadi to lalle a sani cewa game da bayyanarsa akwai hadisai ingantattu yanki mai girma daga cikinsu isnadinsu ingantattu ne. “Kuma shi Albani yana daga masu bayyana tawaturancinsa[27].”
Za mu wadatu da wannan gwargwadon saboda takaitawa kana cewa wasu daga cikin masu bincike sun tabbatar da ikrarin malamai da masu nazari da dama game da ingancin hadisai game da Mahadi wadanda adadinsu ya kai ikrari sama da sittin.
Malaman ilimin hadisi da dama da kwararru a kan ilimin hadisi da koyarwa sun ambata a sarari game da tawaturancin hadisan Mahadi a littafan Ahlussunna da Sahihai da lsnadai da wasunsu saboda la’akri da yawan da suke da shi za mu takaita ne kawai a kan wasunsu su ne:-
1- Al Barbahariy shaihin ’yan mazhabar Hanbaliyya kuma babbansu a zamaninsa (wafati shekara ta 329 Hijiriyya) shaikh Hamud Tawijiri ya kawo daga gare shi a cikin littafin sa mai suna:
“AL lhtijaj bil Asar ala man ankaral Mahadi AL-Muntazar” shafi na 28 cewa ya ce a cikin littafinsa (sharhis sunna) “Al-lmanu bi nuzuli lsa Bin maryam (A.S.): Zai sauko ya yi salla a bayan Al-Ka’im daga zuriyar muhammadu (S.A.W.A.) kuma ba zai boyu ba cewa lmani yana nufin kudurcewa a zuciya, kudurcewa kuwa ba a gina shi a kan hadisin yan daidaiku.
2- Muhammad Binul Husainil Abiriy As-Shafi’iy: ya ce a cikin littafinsa manakibu shafi’i: “Ya zo a jejjere ta hanyoyi dabam-daban a hadisai kuma maruwaitansu da dama sun ruwaito daga Mustafa (S.A.W.A.) dangane da zuwan mahadi cewa yana daga zuriyar gidansa ne (S.A.W.A.) kuma zai yi mulki na tsawon shekara bakwai kuma zai cika duniya da adalci, kuma Annabi lsa (A.S.) zai bayyana tare da shi ya taimake shi a kan kashe Dujal.”
Kuma ya kawo wannan ma daga kurtubiy malikiy a littafin Tahzibil kamal 25: 146 da 181a littafin maruwaita na Muhammad Bin Khalid Al-Jundiy, da kuma lbinul Kayyim a littafin Al-manarul munif: 142/ 327 da dai sauransu.
3- Kurtubiy malikiy (wafati shekara ta 671 Hijiriyya) ya kawo maganar A bariy wadda ta gabata kuma ya karfafa shi da abinda ya kawo na daga hadisai game da Mahadi (A.S.) ya kuma kafa hujja da maganar Imam Hafizul Hakim Naisaburiy, “Hadisai daga Annabi (S.AW.A) game da bayyanar Mahadi (A.S.) da kuma cewa daga cikin zuriyarsa ne kuma daga ’ya’yan Fatima ne tabbatattu ne.[28]”
A cikin Tafsirinsa kuma (Jami’ul Ahkamul kur’an) ya ce “Hadisai ingantattu sun zo ta hanyoyi dabam-dabam da dama dangane da cewa Mahadi daga zuriyar manzo (S.A.W.A.) ne[29].”
4- Hafiz mutkin Jamaluddin maziy (wafati shekara ta 742 Hijiriyya) ya kafa hujja da maganar Abiriy wanda ya gabata dangane da zuwar hadisan ta hanyoyi dabam-daban game da Mahadi (A.S.) bai kuma kawo wani abu da ke nuna wata tababa game da su ba ya dai kawo su ne kawai a zube abinda ke nuna cewa al’amari ne da aka sallama game da shi[30].”
5- lbinul Kayyim (wafati shekara ta 751 Hijiriyya) ya karfafa shi da maganar Abiriy da ta gabata dangane da hadisan Mahadi da suka zo ta hanyoyi dabam-daban ya yi haka ne kuwa ta hanyar rarraba hadisan game da Mahadi ne zuwa kashi hudu sahih, ingantacce da kuma Hasan,mai kyau, da Gara’ib ababan al’ajabi da kuma maudhu’at, wadanda aka[31] kaga kuma ba zai zama boyayye ba cewa tarin sahihan da kyawawan na daga cikin abinda ya kai matsayin mutawatir wato wanda ako ruwaito ta hanyayi daban-daban da dama, wanda shakku ba ya zuwa masa saboda yawansu da kuma kakkawo su.
6- lbin Hajaril Askalaniy (wafati 852 Hijiriyya) ya kawo maganar dangane da tawaturan-cinsa da wasunsa, sa’an nan ya karfafa shi da maganarsa cewa: “Acikin sallar Annabi lsa (A.S.) a bayan wani mutum daga cikin wannan al’umma tare da ka-sancewarsa a karshen zamani kuma kusan lokacin tashin duniya-akwai nuni ga ingancin maganar cewa kasa ba ta rabuwa da wani tsayayye na Allah da hujja.[32]”
7- Shamsuddin Sakhawiy (wafati shekara ta 902 Hijiriyya) wasu daga malamai sun bayyana a sarari cewa sakhawiy na daga cikin masu bayyana a sarari dangane da tawaturancin hadisan mahdi (A.S.) daga cikinsu akwai: Allama shaikh muhammad Arabiy Fasiy a littafinsa makasid, da kuma ma’abucin bincike Abu zaid Abdurrahman Bin Abdulkadir Al-Fasiy a mubhijul kasid, a kan abinda ya kawo daga Faizul Gumariy. Daga cikinsu akwai Abu Abdillah muhammad Bin Ja’afar kataniy (wafati 1345 Hijiriyya) a littafin Nizamu lmutanasir minal Hadisil mutawatir: 226 / 289.
8- Suyutiy (wafati 911 Hijiriyya) ya bayyana kasancewar Hadisai game da Imam Mahadi (A.S.) cewa mutawatirai ne a cikin littafin “Al-Fawa’idul mutakasira fil Ahadisil mutawatira da kuma takaitac-censa da ake kira: Al-Azhaarul mutanasira, da wasunsu daga cikin littafansa a bisa bayanin Al-Gumariy Al-shafi’iy.
9- lbin Hajaril Haisamiy (wafati she-kara ta 974 Hijiriyya) yana kariya ga akidar musulmai da bayyanar Imam Mahadi sau dayawa ta hanyar bay-yana ruwaito hadisan ta hanyoyi dabam-daban.[33]
10- Muttakiy Hindiy (wafati shekara ta 975 Hijiriyya) wato marubucin littafin kanzul ummal, shi muttakiy Hindiy ya yi kariya kwarai ga akidar Imam Mahadi (A.S.) yana dogara da hujjoji da dalilai a cikin littafinsa: Al -Burhan Fi Alamati Mahdi Akhiriz Zaman”.
La’alla mafi muhimmancin abinda ke cikin wannan littafi shi ne fatawoyi hudu kebantattu game da wanda ya karyata bayya-nar Mahadi: Fatawoyin su ne: Fatawar lbin Hajaril Haitamiy As-shafi’iy da kuma Fatawar sheikh Ahmad Abis surur Binus saba Al-Hanafiy, da kuma fatawar sheikh yahya Bin muhammad Bin Hanbaliy.
Muttakiy ya kawo nassi a kan cewa su wadannan malaman su ne ma-laman mutanen makka kuma malaman mazhabobi hudu, kuma duk wanda ya duba fatawoyinsu ya sani sani na yakini cewa su sun yi ittifaki a kan cewa hadisan Mahadi mutawaturai ne, da kuma cewa wanda ya karyata su ya wajaba ya sami horo sun ma bayyana a sarari cewa wajibi ne a masa bulala a kuma ladabtar da shi a muzanta shi har ya koma zuwa ga gaskiya ko ba ya so kamar yadda suka bayyanaidan ba haka ba to a zubar da jininsa.[34]
11- Muhammadu Rasulul Barzanji (wafati shekara ta 1103 Hijiriyya) ya bayyana tawaturancin hadisan Mahadi (A.S.) a sarari yana cewa: “Hadisai game da samuwar Mahadi da kuma bayyanarsa a karshen zamani da kuma cewa daga zuriyar manzon Allah (S.A.W.A.) yake daga’ ya’yan Fatima (R.A.) sun kai gwargwadon mutawatir, wandaaka ruwaito ta hanyoyi dabam daban masu dama, a ma’ ana kuma babu wata ma’ ana dangane da musa su.”[35]
12- Sheikh Muhammad Bin kasim Bin muhammad Jasus (wafati 1182 Hijiriyya) kattaniy ya kawo a littafin NazmuL mutanasir ya bayyana cewa mutawaturi ne.[36]
13- Abul Ala’l lrakiy Al Fasiy (wafati shekara ta/ 1183) yana da littafi game da Imamul Mahadi, kuma ya kawo a cikin littafin Nazmil mutanasir cewa hadisai game da Mahadi mutawaturai ne.
14- Shaikhul Safariniy Al-Hanbaliy (wafati 1188 Hijiriyya) Al-kanuji ya kawo daga gare shi cewa shi yana daga cikin masu cewa hadisan Mahadi (A.S.) mutawaturai ne, a lattafinsa mai suna Allawa’ih[37].
15- Shaikh Muhammad Bin Ali Al-sabani (wafati shekara ta 1206 Hijriyya) ya kawo batun mutawaturanci daga lbin Hajar a littafin As-sawa’ik da wasunsa ya kuma nuna cewa shi ma na daga maganarsa.[38]
16- Asshaukani: (wafati shekara ta 125 Hijiriyya a shahararren littafinsa (Al-taudhi fi tawaturi maja’a fil muntazar wad Dajjal wal masih) ya wadatar wajen tabbatar da matsayinsa game da tawaturanci Hadisai game da Mahdi (A.S.).
17- Mumin bin Hasan bin mumin As-shabalanji (wafati shekara ta 1291 Hijiriyya) ya bayyana a sarari cewa hadisai game da Mahadi (A.S.) mutawaturai ne kuma shi daga cikin Ahlul Bait yake.[39]
18- Ahmad Zainiy Dahlani mufti shafiiyya (wafati shekara ta 1304 Hijiriyya) ya bayyana a sarari kan cewa Hadisai game da Mahadi (A.S.) na da yawa kuma ya ce “(kuma yawan wadanda suka kawo shi yawan sashe na karfafa sashe har ya kai ga darajar da ke ba da ma’anar hujja tabbatacciya) kuma ba zai boyu ba cewa matsayin tabbatac-ciyar hujja a hadisai na samuwa da tawaturanci.
19- Sayyid Muhammad sadik Al-kanuci Al-Bukhariy (wafati shekara ta 1307) ya ce game da hadisarn Mahadi (A.S.) “Hadisan da aka ruwaito game da shi duk da sabaninsu suna da yawa matuka sun kai matsain mutawaturai.”
20- Abu Abdillah Muhammad Bin ja’farul kattani Al-maliki (wafati shekara ta 1345 Hijiriyya) ya kawo magana game da tawaturanci daga wasu da muka ambata su har ya ce: “kuma abinda yake tabbatacce shi ne cewa hadisan da suka zo game da Mahadi da ake saurara mutawatirai ne”[40]
Da dai sauransu wadanda wannan bayani takaitacce ba zai wadatar ba mu kawo dukan maganganunsu kuma wasu masu bincike sun bi diddiginsu tun daga karni na uku har zuwa wannan zamanin.
A nan babu makawa mu rubuta muhimmiyar kalmar malam Badiuz zaman sa’id An-Nurisiy -wanda yana daga cikin manyan malaman Ahlis sunna a farkon karni na goma sha hudu Hijiriyya, ya ce:
“A duniya baki daya babu wata jama’a mai asali mai albarka mai daukaka da ke daukaka zuwa ga darajar Ahlul Baiti da matsayinusu, kuma a cikinta babu wani taro ko wata jama’a mai haske da ta fi haskakawar jama’ar Ahlul Bait da mutanensu. Na’am lalle zuriyar Ahlul Bait wadanda aka ciyar da su ruhin hakikana Alkur’ani kuma sun shayu daga mabubbugarsa, kuma sun haskaku da hasken daukakar Imanin Musulunci don haka suka ketare zuwa ga kamala, suka samar da daruruwan gwaraje madaukaka, kuma suka kaddamar da dubban ja-goran kyautata zukata domin ja-gorancin Al’umma, babu makawa cewa su suna bayyana wa duniya adalci cikakke da ja-goransu mafi girma Al-Madi Al-Akbar, da kuma hakkinsa na raya shari’ar Muhammadiyya da Kuma hakikanin Furkani Mai rarrabe tsakanin karya da gaskiya, da sunnar Ahmadu da aiki da ita da gudanar da ita.
Kuma wannan al’amari yana cikin matukar abubuwa na hankali ballantana kuma na matukar cikin lazimai da kuma larurai bama haka ba kawai a’a haka ka’idar dokokin rayuwar zamantakewa ya hukunta.
[1]- Tafsirul Kabir na Fakrur Razi Juzu’i na 16 shafi na 40.
[2]- Durrul Mansur Juzur’i na4 shafi na176.
[3]- Tafsiru lbin Jussiy shafi na 252
[4]- Durril Mansur 4: 176.
[5]- Majma’ul Bayan 5: 35.
[6]- Majma’al Bayan 5: 35.
[7]- Tafsirun kurtabiy 8: 121, da Tafsirul kabir 16: Ho, da Majma’ul Bayan 5: 35.
[8]- A duba karin bayani a fasali na uku na wannan littafin.
[9]- Majma’ul Bayan 4: 398.
[10]- Ma’alimut Tanzil, Al-Bagawiy 4: 444 / 61 da Kasshaf 4: 26, Tafsirul Kabir 27: 222 da Tafsirul Kurtabiy, 16: 105, Tafsirun Nafsiy mai Hashiya da Tafsirul Kazan 4: 108-109, da Durural Lakit 8: 24, da Baharul Muhit 8: 25, Tafsiriu Ibin Kasir 4: 142 Tafsiru Abis Sa’ud 8: 52, Mawaridud Dhaman hadisi na 1758.
[11]- Tafsiru Mujahid: 2/ 583.
[12]- Al-Bayan fi Akhbari Sahibiz Zaman: 528.
[13]- Durrul Mansur: 6/ 20.
[14]- Usulul Kafi Juzui na 1: 341/ 22, Kamaluddin 2: 324, B. 23 hadisi na 1, kitabul Gaiba Shaikh Tusi: 101, Kitabul Gaiba Nu’umaniy: 149 B.10 hadisi: 1, Hidayatul Kubra Al Hadhini: 88, Yanabi’ul Muwadda Juzu: na 3: 85, Babi na 71.
[15]- A salinsu dai shi ne Malam Ali wanda ya sanya kimanin littafan Ahulus Sunna talatin a liffafinsa mai suna Imam Mahadi (A.S.), alhali shi kuwa Allama Zabihullah Muhallati Ya kai adadinsu zuwa littafa arba’in, kuma ya sanya da sunayensu da sunayen marubutansu a littafin Mahadin Ahlul Baiti (A.S.) shafi na 18-21 har ila yau kuma a cikin wannan littafin da aka ambata ya ambata jerin sunan wasu littafan daga bangaren Shi’a dangane da Imam Mahadi (A.S.) inda ya kai adadinsu zuwa daruruwan gomomi akwai littafa da dama game da Mahadi (A.S.) wadanda ba ambata a wadannan littafa biyun ba.
[16]- Littafin lbrazul wahamil maknun shafi na 437.
Wannan kenan, bul Faiz yana da wani dan’uwa da aka kidaya shi a cikin malamai ma’abuta Falala a kasar maroko wanda ake yi wa Alkunya da Abul Faizul Gamariy shi ne kuma maeubucin littafin “lmamul Mahadi” kuma ya kara a binda dan’uwansa ya ambata a littafin lbrazul waham da sunaye uku daga sahabbai da kuma biyar daga Tabi’an da suka ruwaito hadisan Mahdi (A.S.) sa’an nan ya tabbatar da lafuzzan ruwa-yoyin wanda ya ambace su daya bayan daya har sai da ya wamnan ya cike abinda ya cike fiye da rabin shafukan littafin 55.
[17]- lbrazul wahamil maknun. Shafi na 438.
[18]- Sunan Tirmizi Juzu’i na 4 shafi na 505 hadisi na 2230da na 2231 da Juzu’i na 4 shafi ha 506 hadisi na 2233.
[19]- mustadrakul Hakim Juzu’ i na 4 Hadisi na 457, 465, 553, da 558.
[20]- mustdrakul Hakim Juzu’i na 4 hadisi na 450, 557, 558
[21]- Mustadrakul Hakim Juzu’i na 4 hadisi na 429 da 442, da 457, da 464, da 502, da 520, da 524, da 557. 4210-4213-da 4215.
[22]- An-Nihaya fi Garibul Hadis wal Asar na Ibin Asir Juzu’i na 5 shafi na 254.
[23]- Minihajus sunna na lbin Taimiyya shafi na 211 Juzu’ i na 4.
[24]- AL-Bayan Fi Akhbari Sahi buz Zaman shafi na 486.
[25]- An Nihayatu FiL Fitani wal malahim na lbin kasir Juau i na 1 shafi na 55.
[26]- An-Nihayatu fil fitani wal malahim Juzu-i na 1 shafi na 56.
[27]- Hawlal Mahadi na Albaniy
[28]- At-Tazkira Juzu’i na 1 shafi na 701.
[29]- Tafsirin kurtabiy Juzu’i na 8 shafi ne 121-122.
[30]- Tahzibul kamal 25: 146 /518.
[31]- Tahzibut Tahzib 7: 125 / 20.
[32]- Fatahul Bariy Fi sharhi sahihi / Bakhariy Jazu’: na 6: 385.
[33]- Sawa’ikul muhrika shafi na 122-126 Fasali na 1Babi na 1.
[34]- Alburhan ala alamatil mahdi Akhiriz Zaman shafi na 178 -183.
[35]- Al lsha’a li ashratus sa’a Al-Barzanji shafi na 87.
[36]- littafin da ya gabata 226-289
[37]- Al-lza’ atu na Al-kanuji shafi na 146.
[38]- As’a furragi bin, 145, 147 da 152.
[39]- AL-Futuhatul lslamiyya Juza’ i na 2 shafi na 211.
[40]- Dafa’u anil kafiy na samir umai diy Juzu’i na 1 shafi na 305-343.