back page

GABATARWA

next page

 

Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin halittu, tsira da Amincci’su tabbata ga mafificin halittansa Annabi Muhammadu da zuriyarsa dadada tsarkakak-ku, da sahabansa masu tsarkin niyya da kuma duk wanda ya bi su da kyak-kyawan aiki har zuwa ranar tashin kiyama. Bayan haka: Tun farkon bayyanar addinin musulunci ya zuwa yau musulmi sun yi imani da ingancin abinda Annabi (S.A.W.A.) ya ba allbishir da shi game da bayyanar mutum daga zuriyar gidarnsa a karshen zamani-wanda ake kira-Mahadi zai cika duniya da daidaito da adalci kamar yadda aka cika da zalunci da ja’irc saboda haka jira da sauraron da muminai suke yi wa Mahadi (A.S.) ya zama na tsawan karnoni babu wanda ya baude ya kauce musu illa ’yan kalilan daga masu da’awar tajdidi da ’canji sakamakan tasirantuwar da suka yi da wasu rubuce-rubucen, masanan Turai yan a sani a gurbata, wadanda ba bincike ba ne a kan abu ayya nanne. Irinsu rubuce-rubucen Fan Flatun da Donald son. da Golad Zihar da Makamantansu ’yan a sani a gurbata wadanda sukeganin sun yi nazarý da bincike na karya kan akidojin musulmi hatta su ka kai ga karyata lamarin bayyanar Mahadi (A.S.) a karshrn Zamani. Wasu na iya zamantowa sun rudu da salonsu na. Kyakkyawar niyya dangane da kira zuwa ga tajdidi da sabunta nazari wajen fahintar al’amuran musulunci da kuma kokarin bayyana dacewarsu da zamantowarsu daidai da manufofin zamani dasuka farlanta wayewa irin ta yanzu, suka ga cewa musanta akidar bayyanar Mahdi martani ne kwakkwara ga kiran Addinin kirista -kunma mai gamsarwa ne ga tafarkin ’yan a sani a gurbata-wadanda suka nufo addinin musulunci suka suranta shi a rubuce-rubucensu da cewu wani kwaure ne da ra-yuwa ba ta bubbuga a cikinsa. Haka nan netasirin darrusan masana Turai ’yan a sani a rusa ya bayyana a kan fahintar wasu daga cikinmu, wanda hakan ya samar da baraka daga ciki, inda zaka ga an shiga yin tawilin tabbatattun adubuwa a addini da kuma sa shakku ga me da wani sashe nasa kamar al’amarin bayyanar Imam Mahadi (A.S.) a karshen zamani kuma mai yiwuwa za ka ji taraddudi mai gundurarwa daga Maganganun ’yan a sani a gurbatan, dangane da alkmarin bayyanar.

Hakan ba za ta taba yiwuwa ba idan ba don dauka mataki ba,ba tare da kyakkyawan nazari ba daga bangaren irin wannan gurguwar fahintar da kuma tasirantuwa da ita har zuwa matsayin imani da cewea ita ce hakika da lalle ne a sallama a mika wuya game da ita duk kuwa da irin dattin da take kunshe da shi da kuma son kan da ke tare da ita wajen daldalewa da kuma yanke hukunci, da makirci ga Musulunci da musulmi, ta yaya ba haka ba alhali kuwa ga Gzolad Zihar da Davi Wir, da Mac Donald da Bandaly, Taw Zie suna bayyana  Cewa Alkur[1] ani na da tuka da warwara.? Babu mamaki mu sami wani daga cikin masu wa’azin addinin kirista ya soki akidar musulmi dangane da bayyanar Imam Mahedi (A.S.) ’duk kuwa da cewa wannan akida ta bayyanar ba wai ta kebantu da Musulmi ba ne su kadai dinsu kamar yadda zai zo a bayanan wannan gabatarwar:

Gamewar Duniya da Akidar Mahadi Lalle akidar bayyanar babban Mai tserarwa wanda zai yada adalci da jin dadi idan ya bayyana akarshen zamani, kuma ya kawar da zalunci da danniya a ko’ina cikin duniya baki daya, ya tabbatar da adalci da daidaito a hukuma mayalwaciya, wannan akida ce da dukan Ma’abuta saukakkun addi-nai ukun nan suka yi imani da ita kuma mafi y’awan alummu suka yarda da ita Yahudawa sun yi lmani da ita, kamar kuma yadda kirista suka yi imani da dawowar Annabi lsa (A.S.) haka kuma Mabiya addinin zordasta sun yi imani da jiran dawowar Brahma shah kazalika kiristan Ahbash suna sauraron dawowar Mai mulkinsu Tiyu’dur tamkar dai Mahadi a karshen Zamani, har ila yau masu addinin Hindu sun yi imani da dawowar Fishino, kamar dai Majusawa dangane da imaninsu game da rayuwar Ushidar. Kazalika zamu iske mabiya addinin Budanci suna jiran bayyanar Ruza kamar yadda Asbaniyawa ke jiran sarkinsu Rusarik da kuma Mangolawa Masu jian ja-goransu Jangizkhan.

An samu wannan akidar a gurin Mutanen Masar tun da dadewa kamar kuma yadda aka samu a dadaddun littafan Mutanen kasar sin. Bugu da kari kuma an samu bayanai karara a gurin hazikan yammaci da Masana Falsafa kan cewa duniya na jiran babban Mai gyara wanda zai ja-goranci al’amura ya kuma hade kan kowa da kowa a karkashin tuta da take guda:

Daga cikinsu akwai: Mashahurin masanin Falsafar nan na kasar Ingila Betrand Russel inda ya ce:

“Duniya na jiran wani mai gyara ya hade kan duniya a karkashin tuta guda da take guda.”[2]

Daga cikinsu akwai: Allama ANESHTYN mai littafin “An-Nazariy Nisbiyya ya ce: “Lalle Ranar da sulhu da Zaman lafiya za su game duniya baki daya Mutane kuma su zama Masoyan juna kuna ’yan’uwan juna baki daya ba shi da nisa[3].

Fiye ma dadukan wannan shi ne abinda Mashahurin Masanin Falsafar kasar ýngila Barnard show ya zo da shi yayin da ya yi bushara da zuwan wani Mai gyara a littafinsa “Man and Super Man”.

Dangane da wannan kuma babban malamin nan Abbas Mahmu Al-Akkad yana cewa a cikin littafinsa “Barnardshw” a karin bayanin cewa: “Ya tabbatagaremu cewa super Man ba abu ne da ba zai yiwu ba kuma lalle kira zuwa gareshi ba zai rasa kanshin gaskiya tabbatacciya[4] ba.”

Dangane da musulmi kuwa dukkaninsa a bisa sabanin mazhobabinsu da kangiyoyinsu sun yi imani da bayyanar Imam Mahadi (A.S.) a karshen zamani a bisa asasin abinda Manzon Allah (S.A.W.A.) ya yi bushara da shi, babu wata Mazhaba da ta kebantu da wannan imani sabanin wata.Malaman Ahlussunna da dama Sun bayyana lmaninsu dangane da akida game da Mahadi tun daga Malaman karni na uku  hijiriyya har zuwa yau cewa wannan al’amari ne da suka yi ittifaki a kansa, kai yana ma daga cikin akidarsu baki daya. Abu da ya fi wannan ma shine Fatawar Malamansu kan wajabcin kashe wanda ya karyata bayyanr Mahadi, wasunsu kuma suka ce wajaba ya yi a ladabtar da shi da dukan da zai luguiguita shi ya wulakanta har sai ya dawo ga gaskiya da kuma daidai a bisa tilas -gwar-gwadan bayani-kamar yadda za mu yi ishara gare shi a bisa asasin fatawoyin da suka fita daga Mazhabobi hudu.

Saboda haka ne ma lbin khaldun ya ce yana mai bayanin akidar musulmi game da bayyanar Mahadi:

“Ka sani cewa  abu da yake mashahuri a tsakanin dukan mabiya musulunci a bisa shudewar zamani shi ne cewa babu makawar bayyanar wani mutum daga Ahlul Bait a karshen zamani wanda zai taimaka wa addini Ya tabbatar da adalaci, kuma musulmi su bi shi, ya shugabanci dukan kasashen musulmi kuma ana kiran sa Mahadi[5]. Kuma Malan Ahmad Amin na Al-Azhar ta kasar masar duk kuwa da tsaurin ra’ayin su biyun game da wannan akida, sa an nan/ Sai ya kara da cewa yana bayyana ra’ayin Ahlussunna, dangane da ita:

“Amma Ahlussunna su ma sun yi imani game da[6] ita.” Sa’an nan kuma Sai ya ambata ainihin abinda ibn khaldun ya[7] ambata sa’an nan kuma yace:

“Ibinu Hajir ya kididdige adadin hadisan da aka ruwaito game da Mahadi, ya iske su sun kai wajen hamsin. Sa’an kuma sai ya am bata abinda yakaranta daga Littafan Ahussunna dagane da Mahadi yece: Na karanta Risalar Malam Ahmad bin Muhammad Rinus Sadik a raddin da ya yi wa lbin khaldun wadda ya sa wa suna “Ibrazul Wahmwato “Bayyana Wahamin da ke akwai daga Maganar lbin khaldun; ya kare maganar lbin khaldun game da sukansa a kan hadisan da suka zo game da Mahadi kuma ya tabbatar da ingancinsu, sa’an nan ya ce: Ai sun kai Matsayin tauwaturi[8]  (hadisi Mai Maruwaita da yawan gaske yadda ba’a kokwantosa).

A wani gurin kuma yana cewa: Na karanta wata Risalar kuma dabam dangane da wannan al’amarin wadda kanunta shi ne:

“Al-lza’atu Lima kana wa ma yakunu baina yadayyis sa’ati “wato” sanar da abinda ya kasance da kuma wanda zai kasance kafin sa’a “wato” Tashin kiyama, na Abi Tayyib din Abi Ahmad Bin Abil Hasanil Hasani”[9]

Har  ila yau kuma ya ce:

“Lalle Imam shaukani ya rubuta littafi dangane da ingancin haka ya sa masa suna’ At-Taudhiu fi tawatri Ma ja’a fil Muntazari wad Dhajjali wal 3 Masihi wato “Bayani game da tawaturancin,(yawan maruwaitan,) abinda ya zo game da wanda ake jira da Dujal da kuma Al-Masihu.” Saboda haka babu bambanci tsakanin shi’a da Ahlussuna game da hadisan imani dangane da bayyanar Mai Tserarwa matukar dai Ahlussunna sun riga sun sami hadisai hamsin game da haka daga tafarkunansu kama sun kidaya bayyanar Mahadi daga cikini alamomin tashin ukiyama, kuma sun tabbatar da bacin maganar lbin khaldun wajen raunana wasu hadisai wadanda suka zo dangane da haka da ya yi, sa’an nan kuma sun rubuta Littafai ko sun yi maganganu wajen raddi a kan haka a kai a kai li ttafai da kuma Risaloli, kai babu ma bambanci tsakanin dukan musulmi da sauran mabiya saukakkun addinai da al’ummu dangane da lmani da asalin koda kuwa sun sassaba a kan ainihin wane ne a ayyane tare kuma da ittifakin musumi a kan cewa sunansa muhammadu ne tamkar sunan Annabi (S.A.W.A.) kuma Lakabinsa a gurinsu shi ne Mahadi. Daga nan ne za a sani cewa ittifakin Ma’abuta sauran addinai da yawancin Al’ummu da kabilu da hazikan yammaci da Masna Falsafa, tare da bambancin addinai, da sabanin akidu, da rarrabar ra’ayoyi da tunani da al’adu -a kan asalin akidar ba zai yiwu ya zamana haka nan babu Madogara ba saboda koruwar tabbatar Makamancin wannan haka sarmadan-ldan kuma muka kara a kan ittifakin da mabiyo mazhabobin addinin musulunci dabam-dabam suka yi baki daya a kan ingancin imani da bayyanarmam Mahadi a karshen Zamani da kuma cewa daga AhliL Bait (A.S.) yake -kamar yadda zai zo filla-filla, to daga nan za a san cewa wannan ittifakin babu makawa ya zamanto yana daga cikin ittifakin wannan al’umma wadda ba zai yiwu ta zamana ta yi shi a kan karya ba, kamar yadda yake tabbatacce a gurin bayaninsa yayin nan kuma sabanin ayyana  ko wane ne shi ba zai cutar da imaninsu da bayyanar Mahadi daga Ahlul Baiti (A.S.) ba , domin akwai yiwuwar sanin hakikaninsa dagalittafan musulmi da ake dogaro da su saboda sanin su da aka yi tan bin hanyar kawo hadisai ta hanyar ji da fada da baki da baki da kuma sadarwa zuwa jigon shari’a da kuma abinda babu kini gare shi na daga tarihin rayuwar al’ummun duniya baki daya

Mu kuma duk da haka muna cewa:

lmanin ma’abuta littafi wato Ahlul kitabi da bayyanar wani mai tserarwa a karshen Zamani ba ya zama nesa da kasancewar addinan nasu sun yi bushara da Mahadi daga Ahlul Bait (A.S.) ba Kamar dai bushararsu game da Annabinmu (S.A.W.A.) sai dai kawai sun boye haka ne saboda taurin kai da girman kai sai dai wadanda suka yi imani da Allah daga cikinsu kuma suka ji tsoron Allah.

Abinda ke cikin littafan Attaura game da busharar bayyanar Mahadi a karshen zamani, kamar yadda nassin abinda Marubucin nan Abu Muhammada odan ya rubutaa a littafin “safaru Armiya”ga dai nassinsa kamar haka:”ku hau ya ku dawakai ku motsa ababan hawa domin zaburar da jaruman kaushada kauda masu kamawa... da kuma Diyun mai rike kwari, wannan ranar shugaban rundunoni, ranar narko domin ramuwar gayya a kan maki-yansa,sai takobi ya ci ya koshi/... domin shugaban rundunoni da aka yanka a kasar Arewa a tekun yufret”[10]  kuma akwai wani abu da ya fi wannan bayyana sosai, sa’id Ayyub masani mai binciken nan malamin Ahlus suna a littafinsa mai suna Al-masihu  Al-Dajjal, ya ce: “ka abi ya ce:An rubuta a As farul Anbiya’: mahdi babu wani aibi a aikinsa”. Sa’an nan sai ya yi karin bayani a wanan nassin ya ce, “Na shaida cewa na sameshi kamar haka a littafan Ahlul kitab suna bin diddi-gin alamarin Mahadi (A.S.) kamar yadda suke bin diddigin hadisai game da kakansa (S.A.W.A.). Hadisan sifrur Ru’ ya sun yi ishara ga wata mace wadda mazaje goma sha biyu za su fito daga tsatsonta sa’an nan ya yi ishara ga wato matar kuma wata wadda za ta haifi mutum na karshe datsaton kakarsa, sa’an nan ya ce: Wannan mata ta kershen hada-rurruka za su dabaibaye ta kuma sai ya sanya alamar hatsarurrukan da za su gewaye wannan matar da sunan “Tannayu ya ce” Tannayu ya tsaya a gaban mata da ke hauare har ta haihu kuma za a hadiye dan nata da zarar ta haihu. Sifrur Ru’uya na 3 sakin layi 12, wato dai hukuma na son ta halaka wannun yaron amma bayan haihuwar yaron, Barkli yana cewa a Tafsirinsa, “yayin da hatsarorin saka dumfaro ta sai Allah ya dauke danta ya  kare shi.” Nassin “Allah ya dauke danta.”

Sifru Ru’uya 1215 wato dai Allah ya boye wannan yaron kamar yadda Barkli yake fada.

Sifru ya ce boyuwar wannan yaran za ta kasance kwana dubu da dari biyu da sittin wannan shi ne gwargwadan lokacin da ke da alama a gurin Ahlulkitab. Sa’an nan game da zuriyar matar baki daya sai Barkli ya ce “Lalle Tannayu zai yi yaki Mai tsanani da zuriyar matar kamar yadda sifru ya ce:

“Sai Tannayanu ya fushi da matar sa’an nan ya tafi don ya shirya yaki da sauran zuriyar ta wadanda ke kiyaye Wasicin Allah.”[11] Sifru Ru’uya na 12 shafi na 13.

Wannan kuma koda yake, bai inganta ba ga Musulmi ya kafa hujja da abinda ke cikin littafan tsoho da saban alkawari saboda irin gurbatawar da kuma Musanyawar da aka yi Musu saidai kuma duk da haka yana tabbatar da Masaniyar Ahlul Kitabi game da Mahadi a sarari, sa’an nan kuma Sabaninsu dangane da cewa wane ne shi a ayyane, domin ba dukan abinda musulunci ya zo da shi bane ya Zama ya kebanta da shi daga addinan da suka gabata aa akwai alamura da dama na asasi Wadanda Musulunci ya zo da su Kuma Sun kasance a shari’un da suka gabata kafin shi.

Shatibi ya ce: “Ayoyi da dama da aka ba da labari a cikinsu game da hukunce-hukunce na asasi a addinan da suka gabata suna cikin Shari’armu kuma babu bambanci a tsakaninsu.”

Ldan har haka ya tabbata to imanin Musulmi game da ingancin abinda Manzo (S.A.W.A.) ya yi bushara dangane da bayyanar Wani Mitum daga Zuriyarsa a karshen zamani kuma har ila yau Wannan akidar ta kasance a gurin Ahlul kitab (wato yahudu da Nasara) ko kuma Wasunsu da suka gabaci addininsu kuma hakan ba Zai fitar da shi daga da’irar addinin Musulunci ba bayan Annabi (S.A.W.A.) ya yi bushara da shi bayan kuma yin imani da cewa shi Annabi (S.A.W.A.) “Ba ya Magana a bisa son rai ba kome ba ne illa wahayi da aka yi.[12]

Amma dangane da imanin aliummu dabam-daban game da ainihin wannan akida kamar yadda ya riga ya gabata za a iya fassara shi a bisa asasin cewa akidar bayyanar Mai tserarwa ba ta saba da dabi’ar Mutum da damuwoyinsa da hanga-hangensa ba. lban da Mutum ya yi tunani koda dan kadan dangane da ittifakin yawancin al’ummu game da ainihin akidar to lalle da ya fahinci cewa akwai hikima mawadaciya wajen tafi da wannan duniyar wadda mutum Zai nemi karin karfi daga gare ta Wajen tabbata da tsayiwa daidai a gaban fandarewar da yake gani da kuma Zalunci da dagawa, kuma ba zai bar debe tsammaninsa ba batare da ya yi guzuri da Sa tsammani da kyawun fatan cewa adalci lalle ne ya yi rinjaye ba.

Amma sabanin Maabuta addinai magabata kuwa da kuma alummun da suka gabata wajen tantance sunan wannan Mai tserarwa, babu wata dangantaka da yake da ita a kan musa abinda Annabi (S.A.W.A.) ya yi bushara game da shi. kuma babu Wani abu da zai sa a yi bayanin rashin daidai dinsu game da ayyana wane ne shi wannan Mai tserarwar matukar dai addinin musu-lunci ya riga ya dauki nauyin wannan al’amari mai muhimmaci, ya bayyana sunansa, girmansa, da zuriyarsa, da  siffofinsa, da rayuwarsa, da alamun bayyanarsa da hanyar hukuncinsa, har ma hadisai masu hanyoyi dabam daban dangane da haka suka zo da adadin maruwaitansa daga bangaren Ahlussunna wadanda suka ruwaito hadisan sun kai sama da sahabbai hamsin kamar yadda manyan malamansu da mahaddatansu da masanan fikihunsu da hadisansu suka bayyana kuma za mu kawo  hujjoji a kan haka daga bisani.

Amma dangane da sabanin musulmi kuwa game da ayyana ainihin sunan Mahadi (A.S.) kamar yadda yake sananne tsakanin Ahlussunna da shi a to babu Wata hujja kome kankantarta kuwa asbilo da wannan sabani  ga masanan Turai da ’Yan Korensu, sai dai ma akasin haka, daga dalilai kwarara akan haka  Dominwannan irin sabani shigen sabani ne akan sanin wasu lamurra dangane da wani abinda babu kokonto cikin tabbatarsa. kamar dai sabaninsu a kan Alkurani game da cewa shi dawwamamme ne ko fararre daga Allah, duk kuwa da cewa sun yi imani da kafircin wanda ya musa shi. To ka kintata wannan a kan sauran  sabanin da ke akwai a sauran al’amuran akida ba jigonta ba.

 

  

Tuka da Warwara game da Shaci-Fadin Akida dangane da Bayyanar Mahadi

 

Lalle sakamako mai ma’ana game da abinda ya gabata na tabbatar da rudu da tuka da warwarar shugabannin Masanan Turai game da cewa al’amarin Mahadi (A.S.) shaci-fadi ne a karshen zamani. Damin kuwa tatsuniyar da lmani ke yadawa da irin wannan kamar, babu shakka ta zare hankulan masu imani da ita. To ta yaya aka yi ya auku cikin al’umma wadda ta fi kowace al’umma a duniya kamar yadda su Masanan Turai ’yan a bata suka yi ikrari da kansu.

Abin al’ajabi ne cewa masu fadin haka suna ikrari da ci gaban rayuwar Musulunci da daukakarta a tsakanin tsarurrukan rayuwa na duniya baki daya kuma ba sa musa gudummawar musulunci wajen gyara zukatan musulmi daga sauran bidi’o’i da tatsuniyoyi da al’adu tsofafi da ke dushe zukata kuma hankula ke kin su. Kuma ba su waiwayi cewa al’umma kamar wannan ba zai yiwu ta yi ittfaki a kan imani da tatsuniya ba, kuma yawancin abin da wadannan Masanan Turai ’yan a bata suka zata yayin da suka sami akidun magabatansu sun cika da tatsuniyoyi da bata sai ya zamanto ya yi musu nauyi su yi rubutu game da Musulunci wanda ya fi zinariya tsarkaka ba tare da sun gwamutsa shi da wani abu na daga kufensu ba, don haka ne suka sifanta abinda ya zo ta hanyoyi dabam-dabam daga Annabi (S.A.W.A.) dangane da bayyanr Mahadi a karshen zamani da cewa wannan yana daga tatsuniyoyi.

Ainihin Musibar ma ba a nan take ba domin mun riga mun san abinda Alkur’ani ke fada game da su cewa:

 “Kalmar da ke fita daga bakunansu ta girma kuma babu abinda suke fada sai karya”. (Surar Kahfi: 5)

Saidai babbar musibar ita ce wadda ke cikin rubuce -rubucen wanda ya sanya wa kansa rigar sayyid Jamaluddin Afghani, da shaikh Muhammnd Abduh da makamantansu daga masu ja-goran kawo gyara abinda ya taimaka wajen boye hakikaninta, da gaskiyarta wadda babu abinda ya zamanto illa fakewa a karkashin inuwar abokin husuma da neman shiriya daga wanda ya riga ya dulmuye a cikin kogin bata, ba tare da tunanin da ake bukata ba, kuma ba tare da mai da hankali ba zuwa ga abinda ke yin barazana ga gadon da addinin musulinci ya bari ba har kuma yake neman rusa asasin musulunci!

Daga nan ne ya zama wajibi a yi taka tsantsan da wadannan da wadancan, da kuma kiyaye abinda za a watsa, ko a yada, kafin bayyanar dalili mai karfi game da akidar musulmai dangane da mahadi a fasalolin wannan binciken.

Allah na Shiryar da wanda ya so ga hanya madaidaiciya.


 


[1]- Littafn Almustashrikuna wal lslam  na Dokta lrfan Abdulhamid   shati na 17 da Dira satun fil Fikril Falsafi al-lslami Dokta Hismuddin Al-Alusi shafi na 68, da Buhusun Fi kur’anil karim Dokta Abduj jabbar shararab shafi na 52-54, An kawo kamar yadda muka gabetar game da fadin wasu makiya musulunci cewa kur’ani akwai tuka da war wara a cikinsa, to sai da an karyata wannan gargi a wadonnan littattafa da muka ombata.

[2]- Al-Mahdi Maw’ud wa daf’us shubhat anhu Sayyid Abdur Ridha Shahristani Shafi na 6.

[3]- Al-Mahdi Maw’ud wa daf’us shubhat anhu shafi na 7.

[4]- Barnard Show: Abbas Mahmud AL-Akkad shafi na 124-125.

[5]- Tarikhu Ibin khaldun shafi na 555 fasalina 52.

[6]- Almahdi wal Mahdaiyya na Ahmad Amin shafi na 41.

[7]- Aimahdi wal Mahadawiyya shafi na: ll0.

[8]- Almahdi wal Mahdawiyya shafi na l06.

[9]- Al-Mahdi waL Mahdawiyya shafi na 109

[10]- Littafi mai tsrki a kar kashin mahjer Audata mahawish Abu muhammad Al-urduni:155, nassin an ciro shi ne daga Safaru lrimiyau na 36 Shafi na 2-11.

[11]- Al-Masih Al -Aajal na sa’id Ayyab bugu na Wku, shafi na 379-380. Na ce: Mahadi a gurin shi’a shi ne Imami na goma sha biyu daga lmaman Ahlul Bait na farkonsu shi ne Ali lbin Abi Talib (A.S.) kuma hadisi game da Mahadi kuwa gaskiya ne kuma shi daga ’ya’yan Fatima yake kuma akwai tabbacin ingancinsa kuma a bayyane yake an ruwaito shi daga hanyoyi dabam-dabam daga Ahlussunna kamar yadda za mu kawo maka kuma a gurin shi’a shi ne wanda ake haife shi daga ’ya’yan fatima na goma sha biyu, uku daga cikinsu kai tsaye, wadanda su ne Hasan da Husaini da Muhsin, Tara kuma ba kai fsaye ba kuma su ne lmamai tara daga ’ya’yan Imam Husain (A.S.) Amma ’ya’yan Hasan (A.S) Suma daga ‘ya’an Fatima (A.S.) suke sai dai kuma an cire su daga cikin adadi goma sha biyun saboda su ba sa daga cikin lmamai. Kuma wannan ba zai hada da wanda ba lmami ba wato Muhsin domin shi ma Fatima (A.S.) ce ta haife shi kai tsaye’saboda haka ne Malam sa’id Ayyub ya ce: “Wadannan sune siffofin Mahadi, kuma har ila yau sune siffofinsa a gurin shi’a lmamiyya masu bin lmamai goma sha biyu.” Sa’an sai ya yi karin bayani a gefen shafi na 379 da abinda da ke ishara ga kusacin siffofin. Wannan kuwa koda yake abu ne mai yiwuwa sai dai imanin shia da wasunsu dangane da bayyanar Mahadi (A.S.) a karshen zamani bai zamanto a bisa asasin littafan tsoho da sabon alkawari ba ne kamar yadda za mugani filla-filla a wannan littafin.

[12]- Surar Najmi 53: 3

Home page