FASALI NA HUDU |
Hakika masu musun Imam Mahdi da wadannan sifofi da muka sifanta shi da su-wato cewa sunansa Muhammad kuma shi dan Imam Hasan Al-Askari ne-to masu musunsa mutane ne wadanda suka yi nesa daga tafarkin musulunci wajen kira zuwa ga imani da akida, domin kuwa tafarkin musulunci kamar yadda ya ginu akan ilimi da hankali, to yana kuma dogaro akan fidira da gaibi.
Imani da gaibi kuwa abu ne wanda yake sashe ne na akidar mutum musulmi domin kuwa ya zo sau da yawa a cikin kurani da sunna inda aka kira musulmi zuwa ga haka. Allah ta’ala ya ce:
(Çáã Ðáß ÇáßÊÇÈ áÇ ÑíÈ Ýíå åÏì ááãÊÞíä ÇáÐíä íÄãäæä ÈÇáÛíÈ)
“A.L.M”. “Wancan littafi, babu shakka a cikinsa, shiriya ne ga masu takawa, wadanda suke yin imani da gaibi…” Suratul Bakara ayata 1-3 kuma Allah Ta’ala ya ce:
(Êáß ãä ÃäÈÇÁ ÇáÛíÈ äæÍíåÇ Çáíß)
“Wadannan daga labaran gaibi ne da muke wahayinsu zuwa gareka”suratu Hud aya ta 49 sannan a cikin sunna akwai daruruwan ruwayoyi wanda ke takidi kan imani da gaibi da kuma gaskata abinda manzanni da Annabawa suka bada labarinsa. Kuma shi yin imani da gaibi idan musulmi ya karyata shi, to imaninsa bai inganta ba, shin hankalinsa ya gane abin dalla –dalla ya kuma san sirrinsa, koko a’a, misalinsa shine imani da mala’iku da aljannu da azabar kabari da tambayar mala’iku biyu a kabari, da dai ire –irensu daga abubuwan gaibi wadanda kur’ani ya ambace su, ko kuma Annabinmu Annabi Muhammad (S.A.W.A.) ya bada labarinsu, sannan maruwaita amintattu wadanda aka yarda da su suka ruwaito mana.
To daya daga cikin irin wadannan labarai, bil hasali ma daya daga cikin muhimmansu shine lamarin Imam Mahdi, wanda zai bayyana a karshen zamani domin ya cika kasa da adalci da daidaito, bayan an riga an cika ta da zalunci da ja’irci.
Hakika Mahdi dai littafan sihah da Musnad sun ambace shi, don haka ba dama musulmi dai yayi musunsa, saboda yawan tafarkunan hadisan da amincin maruwaitansu da dalilai da alamomi da tarihi ya nuna dangane da Mahdi kansa, kamar yadda muka tabbatar a cikin wannan littafi .
A dalilin haka ne zaka ga cewa masu musun Imam Mahdi, shin koda wadanda maganganun mutan yamma da kuma kafirai mazowa Gabashi yayi tasiri akansu, ko kuma wadanda suka gaji kiyayya da wannan lamari daga magabatansu, to zaka ga cewa tun da suka ga cewa sun rasa hila da dabara sun kuma rasa abinda zasu yi dangane da wadannan dalilai masu yawa da hujjoji bayyanannu da kuma ikrari masu yawa kan Imam Mahdi –sai suka koma ga kirkiro wasu shubuhohi marasa kan gado, suka kuma koma ga yin wasu tambayoyi na batarwa, ba don komai ba sai domin su ga sun hana al’ummar musulmi aiwatar da wajibinta dangane da abinda ya rataya a wuyanta lokacin sauraron bayyanar Imam Mahdi cewa suka yi wai tsawon shekarun Imam Mahdi ya saba ma hankali da ilimi. Mu kuwa zamu bayyana wa mai karatu a fili cewa wannan magana tasu yasassha ce, ba karbabba bace a ilmance da kuma a hankalce da kuma mizani na gaskiya.
Watakila muhimman tambayoyin da suke ambato sune, abinda ya shafi karancin shekarun Imam da dogon zamaninsa da amfanin buyarsa a gare shi da kuma yadda a’lumma zata amfana da shi alhali yana boye.
TAMBAYA TA FARKO: yaya aka yi ya zama lmami alhali yana da shekara biyar da haihuwa? AMSA: Hakika Imam Mahdi A.S. shine khalifar babansa kan Imamancin al’umma, wannan yana nufin kenan, shima Imami ne cikakke, ciki da waje yana kuma da dukan abinda lmamanci ya kunsa na tunani da tsarkakan zuci, tun yana dan kankani sosai a ruyuwarsa mai albarka.
Shi kuwa yin Imamanci tun yana yaro abu ne wanda wasu daga cikin iyayensa suka riga shi yi, domin kuwa Imam Jawad, Muhammad bin Ali (A.S.). ya zama lmami tun yana da shekara takwas da haihuwa, sannan kuma Imam Ali bin Muhammad Al Hadi (A.S.) shi kuma ya zama Imami yayin nan yana da shekara tara da haihuwa, Imam Abu Muhammad Al-Askari (A.S.) wato mahaifin Imam Mahdi, shi kuma ya zama lmami a yayin nan yano da shekara ashirin da biyu da haihuwa. To idan aka duba za a ga cewa lmamanci tun ana yaro abu ne da ya kai tsororuwarsa a lokacin Imam Mahdi da Imam Jawad. Wannan kuwa abu ne wanda wasu iyayen Imam Mahdi suma suka yi shi, kuma musulmai suka gani da idonsu suka kuma fahimce shi tare da lmamai, to wani dalili ne ya fi wannan karfi, ace abu ya faru kuma al’umma ta gani, to ga bayaninsa:
1- Shugabancin Imami daga Ahlul Bait (A.S.) ba irin na sauran masu mulki bane wanda ke zama a fadar mulki sannan sarautarsa ke isa ga ’ya’yansu ta hanyar gado, hukumar zamani kuma ta kare su, kamar shigen hukumar Banu umayya da Banu Abbas da fatimiyyun, a’a, su Ahlul Bait lmamancinsu kan sami karbuwa wajen mutane ne, ta hanyar tasirin da sukan yi a ruhi da zuciyan mutane, da kuma hanyar ilimi da tunani, wanda ta wadannan hanyoyi ne mutane da kansu sukan gane cewa lallai wadannan su suka cancanci lmamanci da shugabancin al’umma.
2- Wannan alaka tsakanin lmamai da al’umma, ta kafu ne tun a farkon musulunci sannan ta bunkasa a zamanin lmamai biyu wato Imam Bakir da Imam sadik (A.S.), har ya zamanto cewa makarantar da wadannan lmamai suka kafa a cikin al’umma ta zama aiki na ilimi wanda ya watsu sosai a duniyar musulmi, abinda ta kunshi daruruwan malaman fikihu da na akida da masu tafisiri da kuma fannoni dabam –dabam na ilimi a musulunci da zamani a waccan lokaci. Dangane da wannan makaranta Hasan bin Ali Alwassha yake cewa:
Hakika na tarar cikin wannan masallaci wato masallacin kufa da shaihunnai dari tara, kowannensu yana cewa Ja’afar bin Muhammad ya bani labari (wato na ruwaito daga gare shi).[1]
3- Sharuddan da wannan makaranta da kuma mabiyanta suka yi imani da su dangane da lmami, wanda kuma dole ne a same su tare da Imam daga bisani a san cancantarsa ga wannan lmamanci, to hakika wadannan sharudda da aka gindaya su a wannan makaranta sharudda ne masu tsanani, domin kuwa ta yi imani da cewa mutum baya zama lmami har sai ya zamanto ma’asumi wato wanda baya laifi, kuma sai ya zamanto shine yafi dukkan malaman zamaninsa ilimi.
4- Wannan makaranta ta kasance tana sadaukar da ababe masu yawa da ita da mabiyanta domin ta ga cewa ta tsaya kyam akan wannan akida nata kan Imam, domin ita wannan makaranta a idon masu sarauta na zamanin, ta zama a matsayin abokiyar gaba ce a garesu, koda kuwa ta hanyar tunani don haka su masu mulki na lokacin suka yi ta kai masu hare-hare, suna kuma azabta su, aka kashe wadanda aka kashe aka kuma daure wadanda aka daure a gidan yari, daruruwan mutane suka mace a karkashin duhun dauri da azaba.Wannan yana nufin cewa yin imani da lmamai abu ne wanda ke jawo musu sadaukarwa mai yawa sannan babu wani abin kwadaitarwa a jiki face abinda wanda yayi imani da su ke nema na kusaci zuwa ga Allah da samun yardan Allah.
5- Su wadannan lmamai da mabiyansu wato yan shi’a suka yi imani da su, suna tare da mutane a kullum, basu zama irin masu kebe kansu daga talakawa ba, su zauna cikin benaye kamar yadda masu mulki ke yi da talakawansu, don haka su wadannan lmamai basu boye kansu daga jama’a, saidai shugabanni masu mulki, su boye su a fursuna ko kuma su tura su hijira na tilas, wannan kuwa abu ne da za mu san shi ta hanyar maruwaita masu yawa da masu hadisi daga abinda suka ruwaito kan kowane lmami daga lmamai goma sha daya iyayen Mahdi (A.S.) da kuma ta hanyar rubututtukan da aka samu na tsakanin lmamai da mutanen zamaninsu da kuma tafiye-tafiye da lmamai suke yi da watsa wakilansu da sukan yi a wurare dabam-dabam cikin duniyar musulmi, har ila yau da irin ziyarce-ziyarce da ’yan shi’a suka saba yi ga lmamansu a garin Madina-tul Munauwara yayin da suka je aikin haji a wuraren nan masu tsarki, to irin wadannan abubuwa sun haifar da dangantaka yau da kullum tsakanin lmamai da mabiyansu a dukan sassan duniyar musulmi baki daya, malamai da wadanda ba malamai ba.
6- Hakika masu shugabancin da suka yi zamani da lmamai, sun zamanto suna kallon lmamai da irin shugabancinsu na ilimi da ruhi, a matsayin wani hadari babba ga mulkinsu da shirye –shiryensu, don haka ne suka yi iya kokarinsu domin su ga sun kawar da wannan shugabanci na lmamai koda yake ita kanta hukuma ta sha zargi akan irin wannan aiki nata Wani lokaci zaka ga hukuma ta nuna rashin tausayin ta ta kuma hada da hanyoyi na zalunci da kekasan zuciya domin neman ta ci gaba da mulkinta, da haka hukuma ta ci gaba da kame lmamai tana daure su duk da cewa yin haka yana jawo mata kiyayya da rashin yarda a wurin musulmai musamman wadanda ke nuna biyayyarsu ga lmamai, koda kuwa malamai ne ko jahilai.
To idan muka yi la’akari da wadannan abubuwa shida da muka ambata wanda suka zama gaskiya ce da ta auku a tarihi babu shakku akansu, zamu iya kaiwa ga sakamako kamar haka:
Hakika yin lmamanci tun Imam yana yaro, abu ne wanda aka yi shi kuma ba demuwa bane, domin kuwa duk Imam da ya fito yana yaro kuma ya ambaci kansa shugaba ga musulmi na ilimi da tunani da abinda ya shafi ruhinsu, kuma a samu cewa mutane su yi masa biyayya a kan lmamancinsa, mutane masu dumbin yawa, to hakika ba makawa a samu cewa shi wannan Imam yana da martaba da daraja na koli a ilimi da sani, sannan yana da masaniya mai yelwa da kuma kudura a kan ilimin fikihu da Tafsiri da ilimin akida da tauhidi, saboda idan da bai zama haka ba, to baya yiwuwa irin wadannan jama’a su yi imani da lmamancinsa. Ga kuma abinda ya gabata na cewa su jama’a suna da dangantaka da alaka da shi Imam a kulli yaumin, kuma jama a sun san irin rayuwar da suka yi kuma sun san su a kurkusa yanzu shin kana ganin yaro zai yi kira ga cewa shi lmami ne kuma ya kafa irin wannan alama ta musulunci akansa, mutane suna ji suna gani, sannan su yi imani da shi, kuma su sadaukar da abubuwa muhimmai da suka mallaka na daga ransu da amincinsu domin sa, ba tare da sun binciki lamarinsa ba, kuma ba tare da cewa lmamncinsa alhali yana yaro ya motsa su ba, domin su nemi hakikanin lamari dangane da wannan yaro wanda ya ce shi Imam ne?
To mu dauka cewa mutane basu motsa ba domin su nemi sanin hakikanin alamarinsa amma kuwa wannan abu zai yiwu ace kwanaki ko watanni ko kuma shekaru su wuce, ba tare da al’amarinsa ya bayyana ba alhali ga irin hulda na yau da kullum dake gudana tsakanin jama'a da wannan yaro da ya ce shi lmami ne? Anya haka na yiwuwa?!
Wai shin hankali zai yadda da wannan abu, ace gaskiyan lamari shine cewa shi wannan Imam yaro ne, a iliminsa da tunaninsa hakkan, amma haka ba zai bayyana ba a tsawon wannan zamani da ake hulda da shi?
To idan mun aza cewa mabiya Ahlul Bait wato shi’ah su basu binciki hakikanin wannan lamari ba, to amma me zai sa hukuma ta yi shiru ba tare da ta nemi ta san hakikanin lamarin ba, idan abin zai amfane ta? Ai wannan kuwa da shine ya fi sauki wa hukuma idan da dai shi wannan yaro da ya zama lmami, yaro ne a tunaninsa da lamurransa kamar yadda yara suka saba? Me yafi wannan nasara a wajen hukuma ace nan take ta kaddamar da wannan yaro a wajen mabiyansa da sauran musulmai a hakikanin sa, ta kuma kafa hujja a kan cewa tun da shi yaro ne to bai cancanci wannan shugabanci na ruhi da tunani ga al’umma ba, Idan akwai wahala a nuna rashin cancantar wanda ya shekara arba’in ko hamsin ga imamanci, to amma babu wata wahala a tabbatar da cewa yaro bai cancanci imamanci ba, komai fahimtarsa da hazakarsa wato irin imamanci wanda shi’a suka yi imani da shi, kuma da wannan hanya shi yafi sauki matuka ga hukuma a maimakon wasu hanyoyi masu wahala da ta bi su, da irin wasu hanyoyi na tursasawa da gallazawa da ta yi ta amfani da su a waccan lokaci.
Fassara daya tak wanda za a iya yi ga shiru da hukuma ta yi dangane da lamarin lmamanci tun ana yaro, shine cewa hukumar lokancin da kanta ta gane cewa shi irin wannan Imamanci tun ana yaro, abu na gaskiya ne hakkan babu rashin gaskiya cikinsa don haka ta yi tsit kan wannan lamari.
Kuma hakikanin lamari shine cewa hukuma ta gano gaskiyar wannan lamari ne a aikace bayan ta nemi ta yi wasa da wannan lamari wato ta jaraba imam, amma sai ta kasa tabbatar da rashin gaskiyar lamarin, tarihi ya nuna mana ire-iren wadannan kokari da hukuma ta yi domin ta tabbatar da rashin gaskiyar wannan lamari amma abin ya ci tura. Amma bamu samu ba koda sau guda a tarihi cewa shi wannan Imam wanda yake yaro ya taba gaza cin jarabawarsu ko kuma sun sa shi cikin halin kaka nikai da irin tambayoyi da suka yi masa, ko kuma sun sa mutuncinsa ya zube a idon mutane!
To wannan shine abinda muke nufi da cewa yin lmamanci tun ana yaro, abu ne wanda ya auku ba sau daya ba a rayuwar Ahlul Bait (A.S.), kuma wannan ba abu bane da bai auku ba. Sannan shi wannan lamari yana da tushensa a da kuma makamancinsa a tarihin addini wanda ya zo a shari’o in sammai da kuma shugabanni da Allah ya zabe su. To ya ishe mu misali kan lmamanci a yaro a shari’ar Allah mu ambaci Annabi yahya (A.S.) inda Allah madaukaki ke cewa”
(íÇ íÍíì ÎÐ ÇáßÊÇÈ ÈÞæÉ æÂÊíäÇå ÇáÍßã ÕÈíÇð…)
“ya yahya ka riki littafi da karfi, kuma mun bashi hukunci yana yaro”[2]
To idan ya bayyana cewa yin imamanci tun ana yaro ba bakon abu bane a rayuwar Ahlul Bait (A.S.) a,a abu ne wanda yayi ta aukuwa, ashe kenan wannan abu bai zan ya jawo alamar tambaya ba dangane da abinda ya shafi rayuwar Mahdi (A.S.) da halifancinsa ga al’umma bayan mahaifinsa yayin da yake yaro.
TAMBAYA TA BIYU: Tsawon rai: Hakika muhimmin abinda suke ta maganarsa a kullum tun a zamanin baya har ya zuwa yanzu shine cewa da suke yi : ldan Mahdi yana nufin mutum ne wanda yake raye kuma yayi zamani da mutanen da suka gabata tun fiye da karni goma sha daya, to ta yaya aka yi ya samu irin wannan tsawon rai? Kuma ta yaya ya tsira daga dokokin da suka shafi dukan halittu, wanda ya shafi kamar tsufa, ta yaya ya tsira ma wannan?![3]
Muna kuma iya yin wannan tambaya ta wata fuska kamar haka: shin abu ne mai yiwuwa ace mutum ya rayu na tsawon karnoni?
To domin amsa wannan tambaya babu makawa mu yi shimfida domin mu yi magana kan “yiwuwa” wato kalmar “lmkan” domin kuwa akwai fassarori uku ko kuma nau’I guda uku ga wannan kalma ta “imkan” wato “yiwuwa” .
NA FARKO: Abinda ake kira lmkanul amali, abin nufi shine abinda ke yiwuwa a aikace kuma an ga yiwuwarsa tabbas a fili, wato ya faru ya kuma yiwu kuma ana ganinsa a sarari.
NA BIYU: Abinda ake kira imkanul ilmi, abin nufi shine abinda ilimi bai kore yiwuwarsa ba, wato ilimi bai hana aukuwarsa ba, a’a shi abu ne mai yiwuwa a ilmance. Kuma ilimi yana ganin cewa abu ne da zai yiwu.
NA UKU: Abinda ake kire imkanul mantiki, abin nufi shine abinda hankali bai kore aukuwarsa ba, wanda hankalin dan Adam bai hana yiwuwarsa ba, a’a a hankalce abu ne mai yiwuwa kuma zai iya faruwa.
To bisa kan wannan yanzu zamu ci gaba kamar haka, zamu fara da yiwuwar abu a hankalce muna masu cewa: shin tsawon ran mutum daruruwan shekaru abu ne mai yiwuwa a hankalce? Wato abu ne wanda hankali ya yarda da shi?
AMSA: E hakika mai yiwuwa ne! lamarin tsawon rai fiye da shekarun da aka saba, har ma da abinda ya ninka shi, bai zama yana cikin abubuwan da basu yiwuwa ba, kuma wannan abu a fili yake idan aka yi tunani kalilan. Abinda yake akwai za a iya cewa wannan abu ne wanda ba a saba da shi ba, kuma ba a gan shi ba. saidai akwai wasu misalai wanda masu tarihi suka ambata kuma wasu rubututtuka suka yada su, wanda idan mutum yayi la’akari da su to ba zai yi musu ba, kuma ba zai yi mamaki ba. To koda an yi mamaki zaka samu cewa da zarar musulmi ya ji muryar wahayi da abinda kur’ani ya fada kan Annabi Nuhu (A.S.) sai mamakinsa ya kau.
(æáÞÏ ÇÑÓáäÇ äæÍÇð Çáì Þæãå ÝáÈË Ýíåã ÃáÝ ÓäÉ ÅáÇ ÎãÓíä ÚÇãÇð)
“kuma hakika mun aika Nuhu zuwa ga mutanensa, sai ya zauna a cikinsu shekaru dubu babu hamsin…” suratu Ankabut aya ta 14. Saboda mu dada yin bayani sosai kan irin wannan yiwuwar, zamu kawo misali kamar haka: ldan da wani ya ce wa wata jama’a cewa ni zan iya haye kogi ina tafiya a kafa ba tare da na yi iyo ba, ko kuma ya ce ni zan iya shiga cikin wuta in fito ba tare da wani abu ya same ni ba, to anan lalle ne mutane su yi mamaki kuma su musanta haka, amma idan ya tabbatar da abinda ya fada a aikace, aka ga ya tsallake kogi yana tafiya a kafa, kuma ya shiga wuta ya fito ba tare da wani abu ya same shi ba, to mamakinsu ko kuma musun da suka yi zai kau. To a wannan hali idan wani ya zo shima ya fadi daidai irin maganar da na farko ya fada, to mamakin mutane ba zai kai na farko yawa ba, haka ma da mutum na uku zai zo ko na hudu ko mutum na biyar, to hakika mamakin da suka yi a karo na farko ba zai zama haka ba a karo na biyar, wato zai ragu sosai, to da haka har ya zama ya gushe gaba daya.
To muma a nan haka zamu ce domin Alkur’ani ya bada labarin cewa:
Annabi Nuhu (A.S.) ya zauna a cikin mutanensa shekaru dubu babu hamsin, kuma wannan bai shafi shekarunsa da suka gabaci annabci ba! kuma Alkur’ani ya nuna cewa Annabi lsa (A.S.) bai mutu ba, saidai gaskiyar zance shine Allah ya daukaka shi zuwa gare shi, kamar yadda ya zo a inda Allah Ta’ala ya ce:
(æÞæáåã ÅäÇ ÞÊáäÇ ÇáãÓíÍ ÚíÓì Èä ãÑíã ÑÓæá Çááå æãÇ ÞÊáæå æãÇ ÕáÈæå æáßä ÔÈøå áåã æÇä ÇáÐíä ÇÎÊáÝæÇ Ýíå áÝí Ôß ãäå ãÇ áåã Èå ãä Úáã ÅáÇø ÅÊÈÇÚ ÇáÙäø æãÇ ÞÊáæå íÞíäÇð Èá ÑÝÚå Çááå Åáíå æßÇä Çááå ÛÒíÒÇð ÍßíãÇð)
“Da fadar da suke: hakika mun kashe Masihu lsa dan Maryam Manzon Allah, alhali basu kashe shi ba, kuma basu kafe shi ba (kere), saidai an kamanta shi ne a gare su, kuma hakika wadanda suka yi sabani a cikin lamarinsa, suna cikin shakku ne game da haka, basu da wani ilimi dangane da shi face bin zato, kuma tabbas ba kashe shi suka yi ba, a’a Allah dai ya dauke shi ne zuwa gare shi, kuma Allah ya kasance mabuwayi ne, mai hikima” Suratu nisa aya ta 157-158.
Har wa yau ya zo cikin sahihaini (Bukhari da Muslim) cewa Annabi lsa zai sauko zuwa kasa, kuma ya zo cikin ruwayoyin Bukhari da Muslim cewa Dujal yana nan da rai.
To don haka yayin da ruwayoyi ingantattu suka yi magana kan cewa Mahdi yana nan, kuma masu shaida suka yi shaida aka kuma sami masu ikrari akan haka, cewa Mahdi daga zuri’ar Manzon Allah (S.A.W.A.) yake kuma daga ’ya’yan fatima yake kuma shi dan Hasan Al-Askari ne an kuma haife shi a shekara ta 255 hijiriyya to don haka babu wani ma’ana ayi musun haka ko ayi mamakinsa, saidai don girman kai da taurin kai.
Ya zo cikin tafisirin Razi cewa: “Wasu likitoci sun ce shekarun dan Adam ba su wuce dari da ashirin, amma wannan aya na kur’ani ta nuna sabanin maganarsu, kuma hankali ya zo daidai da abinda aya ta ce domin kuwa wanzuwar halittar dake jikin mutum abu ne mai yiwuwa akan kansa, idan kuwa ba haka ba, da dan Adam bai kai tsawon shekaru ba. Sannan yana yiwuwa mahaliccin dan Adam ya ci gaba da kare halittarsa har zuwa zamani mai tsawo, domin kuwa shi wanda ke kare halittar dan Adam, idan shine Allah Ta’ala, to Allah Ta’ala madauwami ne –zai kuma iya kare halittar mutum idan kuma mai kare dan Adam wani ne ba Allah ba, to shi ma waccan dole ne tushensa daga Allah yake, to tunda shima tushensa daga Allah ne, to yana iya yiwuwa shima kariyarsa ya zama mai tsawo, a sabili da haka, wanzuwa abu ne mai aukuwa (yiwuwa) akan kansa, idan kuma bai faru ba to saboda wani sababi ne dabam daga waje amma ba daga kansa ba, shi kuwa wannan sababi da ya hana wanzuwa, shi ma abu ne da za a iya rasa shi, don haka ne ma wadannan tsawon shekarun suka yiwu ga Annabawa, domin rasa wannan sababi da aka yi daga waje: da wannan bayani, ya fito fili cewa maganar wadannan likitoci ya saba ma hankali da kuma Alkur’ani da sunna”[4]
Da haka ne Imam Razi ya kafa hujja akan yiwuwar tsawon rai ga mutum fiye da abinda al’ada ta saba gani, kamar yadda ya tabbata a tsawon ran Annabi lsa (A.S.). Kuma daidai wannan dalili ya inganta a kafa hujja da shi akan tsawon ran Mahdi (A.S.). Wani abu da ke karfafa wannan dalili shine ittifakin da littafan sihah da wasunsu suka yi akan saukowan lsa (A.S.) a karshen zamani domin ya taimaki Imam Mahdi (A.S.) kashe Dujal, kuma ka riga ka san amsar tambayar da ke cewa: wanene Imam Mahdi?dalla –dalla.
Yanzu kuma zamu yi zance a kan imkanul Amali-wato yiwuwa a aikace. To ga tambayar da za mu yi, shin irin wannan yiwuwa wato a aikace abu ne da jinsin dan Adan, wato idan aka duba bil Adam baki dayansa, shin irin wannan abu yana iya faruwa a garesu? Amsa: an jaraba irinsa akan zamanin da muke ciki da irin kayayyakin aiki da suke hanun dan adam, da kuma ci gaban ilimi da ake da shi, ya zuwa yanzu, baa ci nasara kan wannan lamari ba, wato ya kara tsawon shekara wa mutane har ya zama ninkin abinda aka saba, sau daya ko sau biyu, wannan abu ne da kowa zai iya gani da kansa, ba sai mun kawo wani dalili a kai ba.
Amma wannan ba abu ne da zai nuna cewa ba zai yiwu dan Adam ya zan yana da tsawon rai ba, domin kuwa duk wadannan kokari da aka yi amma suka ci tura, abu ne da dan Adam wato mutum da kansa ya nemi ya tsawaita ran mutum dan uwansa, saidai kuma ai dama rai yana hanun Allah madaukaki ne. To don haka idan dan Adam ya nemi yayi katsalandan wajen ganin ya tsawaita ran mutum, ba tare da abinda kadara ta ginu akai ba, to wannan ba mai yiwuwa bane.
Saidai kuma shi Allah Ta’ala shine yake samar da sabubba wadanda ke jawo tsawon ran mutane har ya zuwa ajalinsu, kuma abinda ilimi zai iya yi anan shine neman gano wadannan sabubba domin kuwa ba sha’anin ilimi bane ya halicci wadannan sabubba –wadanda suka kebantu da Allah Ta’ala babu jayayya-to akan wannan ne za a fassara yiwuwa ta bangaren ilimi, wato al imkanul ilmi wanda zamu yi tambaya kamar haka:
Wai shin karin tsawon rayuwa ga mutum fiye da yanda aka saba, abu ne mai yiwuwa a ilmance ko kuwa a’a?
AMSA ta farko: E abu ne mai yiwuwa a ilmance, kuma muna da shaida akan haka da kuma dalilai wanda suke karfafa cewa ilimi bai kore yiwuwar haka ba.
1- Hakika gwaje gwaje na ilimi sai dada karuwa suke domin a ga an tsawaita ran dan adam fiye da yadda aka saba, kuma wadannan gwaje-gwaje sai dagewa ake akansu saboda a ga cewa an kawar da tsufa. Yya zo a cikin mujallar Muktataf ta Masar juzu’I na 2 daga lamba ta 59 wanda ta fito a watan August 1921 miladiyya wanda yayi daidai da 26 ga zil kida shekara ta 1339 hijiriyya a shafi na 206 a karkashin babin “Dauwamar mutum a doron kasa”, to ga abinda suka ce: Masani “Raymond paul” daya daga malaman jami’ar JONES HIPKINS a Amirka ya ce: “hakika ya bayyana daga wasu gwaje-gwaje da aka yi cewa gabobin jikin mutum suna iya rayuwa zuwa duk lokacin da aka nema, saboda haka zai yiwu ran dan Adam yayi tsawo zuwa shekara dari (100), kuma watakila babu wani abu da zai hana shi kaiwa tsawon shekaru dubu (1000).”
Kuma wannan mujallar ta ambata a adadinta na 3 na shekara ta 1959 shafi na 239 cewa: “Hakika yana yiwuwa mutum ya rayu na tsawon shekaru dubbai, idan dai wani abu da zai yanke igiyar rayuwarsa bai zo masa ba, kuma wannan fade ta su ba wai zato ne kawai aka fade shi ba, a’a wannan sakamakon bincike ne da jarabce-jarabce suka karfafa shi.
Kuma zamu wadatu da magana kan imkanul ilmi da wannan maganan da muka yi kan yiwuwa ta fuskar ilimi, wanda masana suke aiki tukuru domin su ga sun zamar da shi imkanul amali, wato sun dawo da shi abu wanda ya zama tabbatacce ya faru, kuma a ga faruwarsa a fili.
2- Ya zo kuma cikin wani littafi da aka buga shi baya-bayan nan da sunan “Haka’iku Agrab minal khayal” Wato gaskiya da ta fi zato bada mamaki, a juzu’I na farko shafi na 24 bugun muassasar lman a Beirut da Daru Rashid a Dimashk to ga abinda ya zo ciki: “BIRIRA ya mutu a shekara ta 1955 miladiyya a kasar sa ta asali Montrea yana da shekara 166 da haihuwa, kuma abokansa sun bada shaida akan shekarunsa da kuma masu rubuta suna a rajista a garin da yake. Shima kansa yayi shaida akan shekarunsa, yayin da ya tuna yakin da aka yi a karayina a shekara ta 1815! Sannan kuma a karshen rayuwarsa an kai shi New york inda wasu kwararrun likitoci suka duba lafiyarsa, to baicin sun samu cewa bugun jininsa tankar na saurayi yake da kuma lafiyan jijiyoyi, da zuciya mai kyau da kwakwalwa tankar na saurayi, su likitocin sun tabbatar da cewa shi mutum ne wanda ya tsufa sosai sama da shekara 150.
Ya zo kuma a shafi na 23 cewa Thomas Ber ya rayu shekara 152.
Haka kuma sajistani mai sunan, ya rubuta littafi da sunan “Masu tsawon rai” ya ambaci mutane da yawa masu tsawon rai a ciki, kuma a cikinsu akwai wanda suka zarce shekara 500 da haihuwa.
3- Hakika shi kansa wannan gwaje-gwaje da likitoci ke yi domin su san ciwon tsufa da sabubban mutuwa, da kokarin da suke yi na yau da kullum da kuma samun nasara da suka yi domin su tsawaita ran mutum, koda kuwa dan kadan ne, to wannan kansa, shima wani dalili ne akan yiwuwar wannan abu, idan kuwa ba haka ba, to da aikinsu ya zama wasa, sabanin hankali.
To idan muka yi la’akari da wadannan ababe dukaninsu, babu kuma kofa da zata saura a hankalce na mamakin lamarin Imam Mahdi saidai idan kuma shi Imam Mahdi ya riga ilimi, a yayin nan sai yiwuwa ta fuskar ilimi ya dawo yiwuwa a aikace a kan shi Imam Mahdi, tun kafin ci-gaban ilimi ya kai ga wannan a aikace kuma wannan shima babu wani dalili na hankali da zai kore shi, ko yayi musun sa, domin misalinsa shine kamar wanda ya riga ilimi wajen gano maganin cutar kansa. Kuma irin wannan rige, yana da yawa a tarihin musulunci, Alkur’ani mai girma yayi ishara ga irinsu da dama, a inda ya yi nuni ga wasu lamura na ilimi a sama ko kasa da kuma wanda ya shafi dan Adam da sauran halittu, sannan daga bisani gwaje-gwaje na ilimi suka zo domin su dada bayyana haka ga mutane a baya bayan nan. Kuma don menene ma zamu tafi da nisa alhali ga Alkur’ani gaba garemu yana fadin yiwuwar wannan abu a aikace, karara, a dangane da rayuwar Annabi Nuhu (A.S.)?[5]
Ga shi kuma ya zo a hadisan Annabi (S.A.W.A.) inda yayi magana a fili dangane da wasu mutane da suka rayu na tsawon karnoni har ya zuwa yanzu, kamar su Halliru, da Annabi lsa (A.S.) da Dujal bisa abinda Muslim ya ruwaito a sahihinsa a hadisin Jassasa. To menene ya sa muka yi imani da wadannan da muka ambata alhali basu da wani gagarumin aiki ko tasiri sosai game da ci-gaban musulunci face Annabi lsa wanda zai zama mataimaki ga Mahdi, kuma zai zama shugaban rundunarsa kamar yadda ya zo a da yawa daga cikin ruwayoyin bayyanar Mahdi.
Amma kuma menene zai sa wasu su yi musu da ray uwar Mahdi wanda yake da gagarumin aiki irin wannan “zai cika kasa da adalci da daidaito” kuma Annabi lsa zai sauko yayi salla a bayansa[6]
Amsa ta biyu: idan mun aza cewa lamarin tsufa abu ne wanda babu makawa daga gare shi, kuma muka aza cewa tsawaita shekarun mutum fiye da yanda aka saba abu ne da ya saba ma dokokin da suka shafi halittar jikin dan Adam, kamar yadda aka samu, to a yayin nan lamarin tsawon ran Imam Mahdi (A.S.) sai ya zamanto cikin sha’anin mu’ujiza kuma ita mu’ujiza ba sabuwar aba bace a tarihi.
Kuma wannan lamari a wajen mutum musulmi wanda yake daukar akidarsa daga Alkur’ani da sunna, ba abin mamaki ko kuma abin musu bane, domin kuwa zai ga cewa akwai wasu dokokin halitta da suka fi wannan tabbatuwa amma aka dakatar da su, kamar wanda ya faru ga Annabi lbrahim (A.S.) yayin da aka jefa shi cikin wuta mai girma sai Allah ya tserar da shi ta hanyar mu’ujiza, kamar yadda Alkur’ani ya bayyana:
)ÞáäÇ íÇ äÇÑ ßæäí ÈÑÏÇð æÓáÇãÇð Úáì ÇÈÑÇåíã)
“Muka ce ya wuta: ki zama sanyi da aminci ga lbrahim”
Kuma wannan mu’ujiza da ire-irenta daga mu’ujizojin Annabawa da karamomi wadanda Allah ya kebe waliyyansa da su, mun wayi gari yanzu a zamanin da muke ciki, fahimtarsu ya zama abu mai sauki a addini, a sanadiyyar irin ci gaba da aka samu na ilimi wanda malamai suka gano da kayan bincikensu.
Domin kuwa a yanzu mun soma ganin kere-kere da kirkire-kirkire wanda da an bamu labarinsu a zamanin baya sai mu yi musunsu mu ki yarda da su, amma sai ga mu a yau muna amfani da su, muna kuma wasa da su a wani sa’i, kamar telebijin, don kuwa da muna karatawa a cikin ruwayoyi a babin “malahim” cewa “a karshen zamani zai zamanto cewa mutum da ke gabas zai ji ya kuma ga wanda ke yamma…” kuma watakil da wasu sun lissafta shi cikin abinda hankali ba zai yarda da shi ba, sannan ga mu nan muna ganinsa muna taba shi. To bisa ga wannan sai mu ce: musun abu da kin sa wai domin kawai ba a taba ganin irinsa ba ko abinda yayi kusa da shi, to yin haka ba abu ne na hankali ba, kuma ilimi bai yarda da shi ba, matsawar wannan abu a ilmance da hankalce abu ne mai yiwuwa, kuma aka tsai da dalilai da misalai akan haka.
To kamar yadda muka ambata cewa akwai a tarihin musulunci, inda aka yi ishara kan abubuwa na ilimi dangane da sama da kasa, da dan Adam da sauran halitta, to shigen wannan, shine irin hadisai da suka bamu labarin bayyanar Imam Mahdi, wanda kuma wannan abu yayi daidai da irin ababen da wannan zamani namu ya kirkiro.
Hakika ya zo daga Imam sadik (A.S.) cewa ya ce: Hakika mai yunkuri a cikinmu (wato Imam Mahdi), idan ya tashi, sai Allah madaukaki ya karfafa idanu da kunnuwan jama’ar shi’armu, har sai ya zamanto babu gidan waya tsakaninsu da ka’im (wato Mahdi), zai yi magana da su, suna kallonsa, suna jinsa a inda yake”[7]
Me zai sa buyan ya yi tsawo haka?
Wani abinda ake cewa kuma har wa yau shine, wai shin menene zai sa ace sai an tsawaita rayuwar Mahdi (A.S.) ya zuwa wannan haddi har a dakatar da dokokin halitta dominsa ko kuma a bukaci mu’ujiza? Kuma don menene ba za mu yarda da ra’ayin dake cewa: hakika shugabancin bil Adama a lokacin da aka yi alkawari ta yiwu a bar wannan shugabanci ga wani mutum dabam wanda za a haife shi a waccan zamanin, kuma ya rayu da mutan zamaninsa daga bisani ya aiwatar da sakonsa na kawo gyara ba?!
Amsar wannan tambaya idan muka yi la’akari da ababen da muka ambata a baya abu ne bayyananne sosai, domin kuwa Allah madaukaki ya rayar da wasu mutane a nan duniyarmu ko kuma a wani wuri, ya rayar da su rayuwa mai tsawo, wanda ta zarce shekarun da yanzu suka gudana a kan Imam Mahdi Allah Ta’ala kuwa ya yi haka ne saboda wani hikima ko sirri wanda mu bamu san shi ba, ko kuma mun dan san kadan daga ciki, amma ko ta kaka dai mun yi imani, kyakkyawan imani game da haka, to lamarin Mahdi ya zama ka mar wadancan, domin kuwa mu tunda mu musulmai ne, to mun yi imani da cewa Allah Ta’ala baya yin abinda babu hikima a cikinsa, dada mun kuma yi imani da abubuwa na gaibi wadanda aka kafa hujjoji da dalilai akansu, to don haka babu wani cutarwa idan bamu san hikimar dake cikin wata akida ba, daga akidoji, kuma kamar haka ne hukunce-hukuncen shari’a da ayyukan ibada suke, ba lallai bane ace mun san sirrin wasu hukunce hukuncen, da sirrin wasu dokokin ubangiji amma ga shi muna ibada akan haka, haka kuma yake a sauran addinai na Allah da wadanda ba na Allah ba, bil hasali ma haka yake dangane da wasu dokokin yan Adam da suke ma’amala akansu.
To bisa haka, idan muka duba irin dalilai da hujjoji da muka ambata a fasalin da suka gabata kan gaskiyar imani da Mahdi, wanda muka ambaci sifofinsa cewa shine Hujja bin Hasan Al Askari, kuma cewa an haife shi, kuma ya zama lmami bayan mahaifinsa a shekaru biyar da haihuwarsa, kuma cewa yana nan a raye duk da tsawon ransa to idan mun duba wadannan abubuwa duka, zamu tarar cewa sakamako guda wanda dole ne mu isa gareshi shine mu yarda da wannan buyansa mai tsawo, shin mun san sirrin wannan buya ko bamu sani ba, koda yake yana iya yiwuwa mu ambaci wasu hikimomi na wannan buya gwargwadon fahimtar dan Adam wanda take fahimta ce gajeruwa, ko kuma gwargwadon kwakwalen bil Adam, wanda suma kwakwale ne takaitattu. Amma idan akwai wani mutum daga cikin musulmai wanda ba zai iya yarda da mu’ujizar Imam Mahdi dangane da tsawon zamaninsa ba kuma bai san fa’idojin dake tare da samuwar Mahdi ba alhali yana boye, to irin wannan musulmi ya wajaba a gareshi ya gyara akidarsa tun daga farkonta bisa yadda kur’ani da sunna suka ambata da kuma dalili na hankali.
Saboda haka bisa wannan, babu dama mu yarda da daya ra ayin domin dalilai sun nuna mana cewa: “babu yadda za a yi kasa ta wofinta daga Hujja na Allah, koda kuwa na dan lokaci kankane”. To bayan mun yi imani da wannan, shin koda mun san wata hikima daga wannan hukuncin kamar (hikimomi da aka fade su dalla-dalla cikin littafa dangane da wannan) ko kuma bamu sani ba, babu makawa mu yarda da cewa Imam yana nan a raye tun daga haihuwarsa, kuma babu wata kofa da za’a yarda da daya ra’ayin.
Ta yaya ne za a amfana da Imam dake boye?
Sannan daga karshe akwai wata tambaya, wanda watakila tana cikin tunani, tambayar kuwa ita ce, idan Imam Mahdi ya zama haka, to menene amfanin da al’umma zasu iya samu daga Imam wanda yake boye, mutane basu isa gareshi su ganshi?!
AMSA: Hakika mutumin dake lura kuma yake bincike kan wannan lamari ya wajaba tun farko ya lura da hadisai ingantattu wanda ke magana kan bayyanarsa wanda zata zama fuju’an kuma cikin gaggawa ko kuwa yadda wasu ruwayoyi suka ce bagtatan, wato ba tare da an fadi wani zamani ko lokaci ayyananne ba, wannan yana nuna kenan lallai ne kowace jama’a daga jama’ar musulmi kuma a kowane zamani suke su rika sauraron bayyanarsa. Wanda yayi tunani kan wannan lamari, ba zai masa wuya ba ya gano fa’idoji da ababe masu yawa wanda suka shafi wannan al’umma. Daga ciki akwai:
1- Hakika wannan abu ne da zai sa kowane musulmi mumini ya zan yana tsaye akan tafarki na shari’a, kuma ya bi dokokinta ya kuma hanu daga hane-hanenta, ya nesaci zaluntar sauran mutane ko kwace dukiyarsu da hakkokinsu, domin cewa bayyanar Mahdi wanda zai zama fuju’an, ana nufin a yayin nan zai kafa daularsa wato zai yi shugabanci, kuma mulkinsa shine ake yin adalci a cikinsa a karbi hakkin wanda aka zalunta daga azzalumi, kuma adalci zai yadu sosai a lokacin har a shafe zalunci baka ganinsa. Kada wani ya ce to ai shari’ar musulunci da dokarta a cikin Alkur’ani, ya hana zalunci, kuma wannan ya isa.
Domin amsarsa ita ce: Idan mutum ya ji cewa akwai hukuma mai karfi wanda zata hana abu, to wannan yana da tasiri mafi karfi wajen hana aikata laifi, kuma ya zo cikin hadisi ingantacce: “hakika Allah na hana abu ta hanyar shugabanci wanda Allah bai hana aukuwarsa ta hanyar kur’ani ba.”
2- Wannan abu ne dake kira ga kowane musulmi mumini da ya zama a shirye a kullum domin ya sa kansa cikin rundunar Imam Mahdi, kuma yayi shirin sadaukarwa na koli domin mulkin Imam ya zama ya samu gindin zama sosai, ya kuma yadu a doron kasa, domin a tsayar da hukuncin Allah. To irin wannan abu yakan haifar wa mumini da yanayi na hadin gwiwa da taimakekeniya da hado kai tare da sauran ’yan uwa musulmai domin zasu zama sojoji ga Imam (A.S.).
3- Hakika wannan buya, abu ne da zai iza wanda yayi imani da shi, zuwa ga aikata wajibinsa na yin umurni da kyakkyawa da yin hani kan mummuna to da wannan sai al’umma ta zama ta sami kariya kuma ta himmatu. Domin mataimakan Imam Mahdi (A.S.) ba wai zasu yi sauraro ne kawai su zuba ido ba, ba tare da sun yi umarni da kyakkyawa, kuma sun yi hani kan mummuna ba, domin yin shimfida ga gina babbar daula ta musulunci da shirya mutanenta ya zuwa lokacin bayyanar Imam Mahdi (A.S.).
4- Hakika al’ummar da ta yi imani da Mahdi rayayye wanda ke boye, al’umma ce wadda a kullum tana cikin jin daukaka da girmamawa, ba zata sunkuyar da kai ga abokan gabar Allah ba, ba kuma zata karbi kaskanci ba don dagawarsu da tursa-sawarsu, domin ita a koda yaushe tana sa ran bayyanarsa mai cike da nasara, saboda haka take kin kaskanci da wulakanci kuma take raina dukkan runduna masu girman kai da abinda suka mallaka na tattali da shiri da kuma yawa.
Hakika irin wannan hali zai haifar da lamari mai karfi dangane da yunkuri da kuma dauriya da sadaukarwa, kuma wannan shine abinda ke tsoratar da makiya Allah, da makiya addinin musulunci, bil hasali ma wannan shine dalilin tsoronsu da fargabarsu, don haka ne suka yi kokari tun da dadewa domin su raunana akidar yin imani da Mahdi, kuma suka juya alkaluman ’yan haya domin su sanya shakku cikinta, kamar yadda dama can suka dade suna kago kungiyoyi da jam’iyyu na bata domin su ga sun ruguza addinin musulunci kuma su ga sun hana musulmai sakewa dada kuma su samu su hana musulmai yin riko ga ingantattun akidojinsu, suka kuma ci gaba da kiran jama’a zuwa ga akidoji na bata, kamar yanda suka yi dangane da akidar Babiyya, da Bahaiyya, da kadiyaniyya da wahabiyya.
Wannan kenan, kuma tana yiwuwa mu kara wasu fa’idojin kan wadannan da muka ambata, wato fa’idojin da mutum musulmi zai samu idan yayi imani da Imam Mahdi (A.S.) zai same su dangane da lahira. Na farko daga cikin fa’idojin shine inganta imanin mutum musulmi dangane da adalcin Allah Ta’ala da tausayinsa ga wannan ai’umma, wato Allah bai barta kara zube ba ta yanda debe kauna da fitar da tsammani zai mamaye su domin yanda suke ganin irin nesata da ake yi daga addini, ba tare da ace Allah ya kawo mata wata kafa ta sa rai da fata ba, kan samun cin nasarar addini a doron kasa baki daya a karkashin shugabancin Imam Mahdi (A.S.).
Daga ciki kuma akwai samun sakamako mai kyau da kuma lada akan wannan sauraro da ake yi, domin kuwa ya zo cikin hadisi ingantacce daga Imam Sadik (A.S.): “Mai sauraron lamarinmu tankar wanda ya sadaukar da jininsa a tafarkin Allah ne”.
Daga ciki akwai bin maganar Allah Ta’ala inda yake zancen wasiyyar Annabi Ibrahim (A.S.) ga ’ya ’yansa:
(íÇ Èäí Åä Çááå ÇÕØÝì áßã ÇáÏíä ÝáÇ ÊãæÊä ÅáÇ æÃäÊã ãÓáãæä)
“Ya ’ya’yana, hakika Allah ya zaba maku addini, don haka kada ku mutu lalle, face kuna musulmai.”[8]
Kuma ta gabata ruwayar dake cewa: “wanda ya mutu alhali bai san lmamin zamaninsa ba -kuma lmamin zamaninmu shine Mahdi (A.S.)- to yayi mutuwar jahiliyya.” Kuma daga dukan abinda muka ambata, zamu ga ma’anar maganar nan ta fito fili wato maganar dake cewa: “Hakika kasa bata wofinta daga hujja ga Allah”.
To daga karshe hakika yana daga cikin abinda kafofin watsa labarai na munafukai makiya musulmi suke aiki tukuru su ga sun yi, shine bincike da suke yi daga cikin sahun musulmai ko zasu samu wanda zasu dauke shi su zagaye shi, su ba shi lakabobin ilimi na karya wanda yake matukar nema, ba don komai zasu yi masa haka ba, sai domin su zamar da shi tamkar tsani domin su cimma manufofinsu, kuma su sanya shi ya zama muryarsu a ta hanyar mujalloli ko kuma a wajen tarurruka da ake sukan musulunci da akidojinsa madaukaka. Kuma abokan gaba, basu samun biyan bukatarsu face a jikin mutumin da ya fandare daga kan hanya madaidaiciya, ya zamar da kansa tamkar yaro da ya kai kansa gurin mai raino jahila, wanda zata yi amfani dashi a cikin kowane irin mummunan wasa da ta ga dama, kamar yadda muka gani a yau dangane da kusatar da salman Rushdie da aka yi da kuma makamantansa, domin a kullum sai nema suke su ga gubarsu ta sami hanyar isa ga dukan wani mutum musulmi mai rauni.
Saboda haka ya zama wajibin addini a yi fadakarwa akan irin wadannan miyagun hanyoyi, kuma a wayar da kan musulmi domin su san manufofinsu, su kuma san hadarurruka dake tattare da su, daga bisani kuma a yi rigakafi wa musulunci da imani ingantacce wanda tushen musulunci mai tsarki yayi umarni da shi, wato Alkur’ani mai girma da sunnar Manzo, da kuma makarantar Ahlul Bait, wato zuriyar Manzo (S.A.W.A.).
To don amsa wannan kira da ya zama wajibci na addini, shi ya sa muka rubuta wannan littafi akan Imam Mahdi, wanda ya zama lamari ne na addinin musulunci tsintsa, kuma ya bayyana dalla-dalla cewa yin imani da bayyanar Imam Mahdi a karshen zamani, abu ne wanda yake tattare da gaskata sakon musulunci madauwami, kuma cewa karyata yin imani da Imam Mahdi, yana nufin karyata sakon musulunci ne wanda ya bada labarin bayyanarsa.
Kuma muna ganin cewa a cikin fasali-fasali na wannan littafi, da ya bi hanyar yin bayani a saukake sannan ya ginu akan kwararan dalillai, wato muna ganin a cikinsa akwai abinda ya raba shi da sauran littafai, domin a cikinsa akwai amsoshi ga bukatun kowane mutum musulmi masani, a kowace daraja yake, domin sanin hakikanin lamarin Mahdi wanda ake sauraro, a ra’ayin addinin musulunci da tunanin sa.
Godiya ta tabbata ga Allah bisa shiryarwarsa, tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen Annabawa da Manzanni Muhammad, da kuma alayensa tsarkakku, da sahabbansa masu tsarkin niyya da wanda ya bi tafarkinsu zuwa ranar sakamako.
1417 hijiriyya.
Saboda Muhimmancin littafan addinin musulunci ne Ma’assasar Imam Ali (a.s) da ke nan birnin Kum-Iran ta dauki nauyi fassara littafan zuwa harsuna dabam-daban da kuma bugawa da yadawa domin wadanda ba sa jin harshen larabci su fahinci abinda suka kunsa kana su ji irin dadin da ke cikin fahintar ma’anarsu; daga bisani kuma su amfane su wajen kyautata dabi’arsu da fatan za su zama hanyar fa’idantuwa da su a duniya da kuma lahira.
Mu’assasar Imam Ali
[1]- Rijalu Najashi shafi na 40/ 80 a tarjamar Hasan bin Ali bin ziyad Al wassha.
[2]- Suratu Maryam aya ta 12. Kuma ya gabata a fasali na biyu a lamba ta 5 da ta 8 inda Ahmad bin Hajar Alhaisami Bashafi’e da Ahmad bin yusuf Alkarmani Bahanafe suka yi ikrari cewa Mahdi (A.S.) an bashi hikima tun yana yaro, ka duba can.
[3]- Wannan tambaya an yi ta a littafan akida da dadewa kuma manyan malaman shi’a sun bada amsarta ta fuskoki dabam–dabam, da kuma sabin fuskoki, to mu anan zamu ambaci wasu ne daga ciki.
[4]- Tafsirul kabir na Imam Razi, juzu’I na 25 shafi na 42.
[5]- Ka duba “Bahsun haulal Mahdi” na shahid Mohd Bakir sadr.
[6]- Mutum uku daga wadanda suka yi sharhin sahih Bukhari sun yi ikrarin wannan, kamar yadda muka gabatar dalla-dalla a farkon fasali na uku, to ka duba can.
[7]- Raudatul kafi juzu’I na 8 , shafi na 201 hadisi na 329.
[8]- Suratu Bakara aya ta 132.